Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

  • Ana kyautata zaton cewa zabukan 2023 za su kasance cikin gaskiya, aminci da karbuwa, inji jami'i daga fadar shugaban kasa
  • Wani mai taimaka wa shugaban kasa Buhari, Umar Ibrahim El-Yakub, ya ce shugaba Buhari ya yi bakin kokarinsa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a 2023
  • El-Yakub ya lura cewa shugaban ya yi hakan ne ta hanyar sanya hannu a kwanan nan kan dokar gyaran zabe

Abuja - Babban mai taimakawa shugaba Buhari na musamman kan harkokin majalisar wakilai, Umar Ibrahim El-Yakub, ya ce idan aka amince da dokar zabe, zaben 2023 zai zama mafi inganci da karbuwa.

Jaridar Daily Trust ta ce, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarorin da shugaban ya samu wajen tafiyar da al’amuran kasar nan.

Kara karanta wannan

Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

Shugaba Buhari yayi kokarin kawo sauyi a dimokradiyya
Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi, kuma karbabbe | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa, dokar zabe ta bude wa ‘yan Najeriya sararin fahimtar dimokuradiyya, kana su iya shiga cikin tsarin a dama dasu.

El-Yakub ya lura da cewa an gano matsalolin da suka kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce gyare-gyare daban-daban da aka yi wa dokar ya kamata a yi la’akari da su a matsayin wata hanya ta bunkasawa tare da kare dimokuradiyyar Najeriya da ‘yan Najeriya baki daya sukayi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shi yana cewa:

“Dokar zabe ta kunshi batutuwan da suka shafi gaskiya da rikon amana da kuma tursasa wa alkalan zaben gudanar da aikinsu na samar wa kasar nan sahihin zabe."

Mai taimaka wa shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, duk da cewa shugaban kasar ya yi nazari a kan kasafin kudin 2022 da kuma dokar zabe tare da yin kira da a yi gyara, amma ko kadan bai yi yunkurin tilastawa majalisar dokokin kasar daukar wani mataki ba.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

A wani rahotonmu na baya, jaridar Daily Trust ta ce masu rike da mukaman gwamnati za su sauka idan har Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kudirin zaben da aka kawo masa.

Daga cikin abin da kudirin ya kunsa shi ne duk mai neman kujerar siyasa a 2023, zai yi murabus.

A wannan rahoto, an kawo Ministoci da kuma shugabannin cibiyoyi, ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ake tunanin dole su ajiye mukamansu.

Ana rade-radin cewa irinsu Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Babatunde Fashola, da Chris Ngige su na harin takarar shugaban kasa a karkashin APC a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel