Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

  • Wata kungiya a arewacin Najeriya ta nuna goyon bayanta ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabannin babban zaben 2023
  • Kungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin wanda ke tarin kwarewa wajen tafiyar da lamuran kasar
  • A cewar kungiyar, Jonathan ya rigada ya san yadda abubuwa ke gudana don haka shugabancin kasar ba zai zame masa bakon abu ba

AbujaWata kungiyar siyasar arewa mai suna Northern League of Professionals ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya fi cancanta don dorewar damokradiyyar Najeriya da kuma kawo ci gaba a kasar.

Kungiyar ta ce idan har aka sake ba Jonathan damar shugabantar kasar, zai kai ta ga matakin ci gaba ta hanyar karfafa nasarorin da aka samu a wannan gwamnati mai ci.

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara
Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara Hoto: John Kalapo
Asali: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran kungiyar, Alhaji Mohammed Yusuf Ajiji, jaridar The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Wani bangare na sanarwar ta ce:

“Gwamnati ci gaba ce kuma ita ce ta kai ga gwamnatin Buhari ta ci gaba da kammala wasu ayyuka da aka fara a karkashin Jonathan.
“Ayyuka kamar ginawa da gyara hanyoyin jiragen kasa, gadar Neja ta biyu, gadar Loko-Oweto, titin Legas zuwa Ibadan da dai sauransu duk gwamnatin Buhari ce ta aiwatar da su duk da cewar sun fara aiki ne a karkashin Shugaba Jonathan.
“Wannan misali ne na ci gaba a gwamnati kuma za mu so ganin yanayi inda Shugaba Goodluck Jonathan zai ci gaba daga inda shugaban kasa Buhari ya tsaya domin tabbatar da ganin cewa akwai wadataccen abubuwan more rayuwa da aiwatar da manufofi da tsare-tsare domin magance matsalolin da kasar ke fuskanta. Manufarmu ita ce tabbatar da samun ci gaba mai dorewa ta hanyar ci gaba da aiwatar da shirin ba tare da katsewa ba.”

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

Kungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin zakarar gwajin dafin tabbatar da dimokradiyyar Najeriya wand aba za a taba mantawa da shi ba, wanda ya aiwatar da sauye-sauye da dama a harkokin zaben kasar tare da mika mulki ga abokin hamayyarsa a cikin lumana wanda ba a taba tsammani ba a Afirka.

Alhaji Alajiji ya ce duk cikin masu neman takarar shugaban kasa, babu wanda ke da tarin kwarewa kamar Jonathan wanda ya yi aiki a matsayin malamin jami’a, mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban kasa.

Ya ce Jonathan ne yafi dacewa don hada kan kasar a wannan mawuyacin lokaci da ake da koe-koke daban-daban a fadin kasar, rahoton Inependent.

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

A wani labarin, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu ya kaucewa tambayar da aka yi masa kan ko zai tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

Sai dai tsohon shugaban ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa zabukan da za a yi dukkansu za su kasance sahihai kuma Najeriya ba za ta dagule ba yayin da aka buga gangar siyasa.

Jonathan ya yi magana ne a wajen wani taron manyan tsare-tsare na kwanaki biyu da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta gudanar a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel