Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

  • Matasan APC a arewa sun nuna goyon bayansu ga mika tikitin shugaban kasa na jam'iyyar zuwa yankin kudu maso gabas
  • Haka kuma, kungiyar ta ce Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi shine ya fi cancanta ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Kungiyar ta ce mika tikitin shugabancin kasar zuwa yankin shine zai nuna adalci da daidaito na jam'iyyar mai mulki

Matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a arewa sun nuna goyon bayansu ga kiran da ake yin a jam’iyyar ta mika tikitinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas.

Matasan, karkashin kungiyar ‘Concerned Northern APC Youth Forum’, sun ce bayan tuntubar da suka yi a fadin jihohin arewa 19, sun yanke shawarar cewa jam’iyyar ta mika kujararta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas
Matasan APC a arewa sun ce Umahi ne ya fi cancanta ya gaji Buhari Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Suleiman Liba, ya ce ya zama dole a nuna adalci da daidaito wajen zabar shugaban kasa na gaba, Daily Trust ta rahoto.

David Umahi ne ya fi cancanta ya gaji Shugaba Buhari a 2023

Kungiyar matasan ta kuma nuna goyon bayanta ga kudirin takarar shugabancin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Janairu ne Umahi ya ayyana aniyarsa ta son takarar shugaban kasa bayan wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce ya fada ma Buhari batun son tsayawa takarar kujerar idan jam’iyyar ta mika tikitinta yankin kudu.

Liba ya ce Umahi ne dan takara mafi cancanta da zai gaji Shugaba Buhari saboda tarin nasarorin da ya samu a jihar Ebonyi, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

2023: Idan Baka Fito Takara Ba, Za Mu Ɗauke Ka Rago Kuma Matsoraci, Ƙungiya Ga Atiku

Ya ce:

“Mun gano cancanta a tattare da Injiniya David Umahi don ya gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
“Nagartarsa da nasarorin da ya samu a jihar Ebonyi sun isa kallo ga kowa.
“Muna umartan sauran kungiyoyi a fadin kasar da su hadu wajen marawa kudirin shugabancin David Umahi baya domin shine tabbataccen hanya mai billewa ga Najeriya.”

An fidda matsaya: Jam'iyyar APC ta tura kujerar shugabancin jam'iyya ga yankin Arewa

A gefe guda, mun ji cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tura kujerar shugabancin jam'iyya ga yankin Arewa gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Gwamna Nasiru El-Rufai (Kaduna) da Atiku Bagudu (Kebbi), ne suka bayyana hakan a lokacin da suke amsa tambayar jaridar Daily Trust a wani taron manema labarai da suka gudanar bayan ganawa da shugaba Buhari game lamurran jam'iyyar.

El-Rufai ya ce jam’iyyar ta amince da sauya mukaman da ba kowa akansu a kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ga tsakanin sassan Arewa da Kudancin kasar nan gabanin taron gangamin jam'iyyar APC na kasa na ranar 26 ga Maris.

Kara karanta wannan

2023: Matasa a yankin Kudu sun nace, sun nemi Atiku ya bayyana kudurinsa na takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel