Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

  • An yi ta kira da babbar murya ga tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan kan ya shiga takarar shugaban kasa a 2023
  • Wani mai taimakawa Jonathan ya so dakile yunkurin da wani dan jarida ya yi na jin ta bakin Jonathan kan burinsa na tsayawa takara
  • A ‘yan makonnin da suka gabata, kungiyoyin siyasa da masu fafutuka daban-daban sun yi ta bayyana goyon bayansu ga tsohon shugaba Jonathan

Jihar Legas - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu ya kaucewa tambayar da aka yi masa kan ko zai tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Sai dai tsohon shugaban ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa zabukan da za a yi dukkansu za su kasance sahihai kuma Najeriya ba za ta dagule ba yayin da aka buga gangar siyasa.

Kara karanta wannan

2023: Magoya Bayan Yahaya Bello Sun Yi Wa Ganduje Zazzafan Martani Kan Cewa Arewa Na Goyon Bayan Tinubu, Sun Ce Ya Riƙe Girmansa

Shugaba Jonathan kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jonathan ya yi magana ne a wajen wani taron manyan tsare-tsare na kwanaki biyu da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta gudanar a Legas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, lokacin da aka tambaye shi game da burinsa na takara a 2023, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ikechukwu Eze, ya dage cewa sai dai a yi tambayoyi game da taron da ake yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar rahoton, Jonathan cikin nutsuwa da murmushi ya ba da amsar tambayar ta farko ba tare da bayyana wani bayani kan burinsa na tsayawa takara ba.

Yace:

“Na yi imani cewa zabubbukan da za a yi a Najeriya za su kasance masu inganci. Idan zabe ya zo a kullum ana fargabar cewa kasar za ta dagule amma ka ga kasar tana tsaye daram.

Kara karanta wannan

Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Haske

“Ko a lokacin da nake kan karagar mulki, na samu labarin cewa a 2015 wasu na fitar da 'ya'yansu zuwa kasashen waje amma ba abin da ya faru. Don haka 2023, zata zo ta tafi kuma kasar nan za ta zauna daram.”

Kawu Sumaila kan batun kafa TNM: 'Yan Najeriya za su samu waraka a 2023

Har ila yau game da zaben 2023, tsohon mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin majalisar dokokin tarayya (majalisar wakilai), Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nuna goyon bayansa ga kafa sabuwar kungiyar siyasa ta TNM.

Kawu wanda ya kasance tsohon bulaliyar majalisar wakila, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, a Abuja, inda ya tabbatar da cewar akwai bukatar irin wannan kungiya a siyasar Najeriya, Aminiya ta rahoto.

A cewar Kawu, duk wani abu da zai karfafa dimokradiyyar Najeriya gabannin zaben 2023 abun ayi maraba da shi ne ba tare da la’akari da ra’ayin siyasar mutum ba, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Kawu ya ce:

“A matsayina da dan damokradiyya, ina goyon bayan kowace kungiya da za ta dawo da tsarin damokradiyya da kawo shugabanci nagari daidai da na kasashen duniya kamar gaskiya, adalci, daidaito da zaben lokaci zuwa lokaci."

Dakta Banire: Nan gaba kadan jam'iyyar APC zata tarwatse saboda abu daya

A wani labarin, tsohon mai bada shawari kan harkokin shari'a na APC ta kasa, Dakta Muiz Banire, ya yi hasashen cewa nan bada jimawa ba jam'iyyar zata tarwatse.

Da yake jawabi a cikin wani shirin gidan Radiyo dake jihar Lagos, Banira ya bayyana cewa kowa yasan APC tasaba yi wa doka karan tsaye.

Ya ce duk wata kungiya ko tawaga da take saba wa dokoki, ba zata taɓa yin tsawon rai ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel