Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

  • Gwamnonin jam'iyyar APC za su sanya labule tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata
  • Ana kyautata zaton za su zabi sabon rana domin gudanar da babban taron jam'iyyar wanda da a farko aka shirya yi a ranar 26 ga watan Febrairu
  • Jam'iyyar mai mulki dai na fama da rikicin cikin gida kan tsarin zabar shugabanninta na kasa

Abuja - A wannan makon ne gwamnonin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari za su zabi ranar gudanar da babban taron jam’iyyar wanda da farko aka shirya yi a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Jam’iyyar mai mulki wacce ta gayyaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta domin ta zo ta sanya ido a taronta da za ta yi a Eagle Square Abuja, ta ki siyarwa kowani dan takara fam a yayin da ranar ke kara gabatowa.

Kara karanta wannan

Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC
Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Rikicin shugabanci ya dabaibaye jam'iyyar

Jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida wanda ya ki ci ya ki cinyewa sakamakon yunkurinta na son zabar shugabanninta na kasa ta hanyar bai daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta rahoto cewa a ranar Lahadi, wata babbar majiya ta fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaban kasar zai gana da gwamnonin APC a ranar Talata.

Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce: “Za a yi ganawar a ranar Talata. Wannan shine shirin a yanzu.”

Jam’iyyar wacce ke ta dage taronta tun daga watan Disambar 2020, tana shirin sake dage shi a karo na hudu biyo bayan rashin tsayar da magana daya a tsakanin gwamnoninta 22 kan batun raba kujeru da kuma tsarin zaben.

Yayin da a baya aka tsara mika kujerar shugabancin jam’iyyar zuwa yankin arewa ta tsakiya, da kuma ba wadanda suka cancanta filin fafatawa, a yanzu akwai tsare-tsaren tsayar da mutum daya wanda wakilan taron za su tabbatar da shi gaba daya bisa umurnin gwamnonin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC na shirya dage taron gangaminta zuwa watan Maris

Sai dai, gwamnonin na neman umurnin Buhari kan wanda za a tsayar, inda shi kuma Buhari ya ki tabuka komai.

Wani mai takarar kujerar shugabancin, Sunny Moniedafe, ya koka cewa jam’iyyar na shirin sake dage taron.

Moniedafe ya bayyana cewa tuni ya rigada ya yi hayar dakunan otel kuma ya yanki tikitin jirgi na abokansa da magoya bayansa da za su je Abuja don taron.

Ya ce wasu mutane a jam’iyyar na kokarin buga iko, inda ya kara da cewar APC ba za ta kwasheta da dadi ba.

Sai dai kuma ya ki bayyana sunayen wadanda yake zargi.

Tsohon shugaban Action Congress of Nigeria reshen birnin tarayya, ya ce babu wanda ya tuntubi wani dan takara don yin gamayya.

Wani dan takarar kujerar, Alhaji Saliu Mustapha, ya fada ma jaridar Punch cewa babu dan takarar da zai janye sakamakon shirin yin hadaka.

Ana kokarin mayar da taron watan Maris

Kara karanta wannan

Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

Jaridar Guardian ta rahoto cewa shugabancin riko na jam’iyyar na kokarin ganin an dage taron da makonni biyu zuwa tsakiyar watan Maris amma dole sai ya nemi yardar shugaban kasa a matsayinsa na babban jigon APC.

Wani hadimin gwamna a kudu maso yamma, ya ce:

“Batutuwa irin na fahimtar juna, lissafin hadin kai da kuma shiyya-shiyya za su kasance cikin ajandar idan gwamnonin suka hadu a ranar Litinin. Ubangidana ya riga ya isa Abuja. Babu yadda za a yi babban taron ya gudana a ranar Asabar. Ana duba yiwuwar sa a ranar 12 ga watan Maris."

APC: Zan goyi bayan a zabi zaƙaƙuran matasa a manyan kujeru, Shugaba Buhari

A baya mun ji cewa Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, rana Jumu'a, ya tabbatar wa matasan APC cewa zai goyi bayan zakakurai daga cikinsu su ɗare manyan muƙamai a taron APC dake tafe.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Buhari ya sha alwashin marawa matasan baya su samu mukamai a shugabancin APC na ƙasa a taron 26 ga watan Fabrairu, 2022.

Kara karanta wannan

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

Kazalika Buhari ya umarci shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, su tabbatar an saka matasa masu hazaka a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel