Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023

Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023

  • Wasu tsoffin gwamnonin jam’iyyar APC sun yi ikirarin cewa Gwamna Mai Mala Buni na son a yi taron gangamin jam’iyyar da zaben fidda gwani a rana guda
  • Hakazalika wani tsohon gwamna ya ce gwamnan na jihar Yobe na hakan ne duk a kokarinsa na son ganin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Sai dai kuma, hadimin Buni, Mamman Mohammed, ya yi watsi da ikirarin inda yace ubangidan nasa na kokarin gyara jam’iyyar ne kawai

Wani tsohon gwamnan wanda ya kasance cikin wadanda suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zargi Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe da son a yi taron gangamin jam’iyyar da zaben fidda gwanin shugaban kasa na 2023 a rana guda.

Da yake martani kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki kan taronta, tsohon gwamnan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki saboda ra’ayin APC, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

Bayan an kai ruwa rana, jam’iyyar mai mulki ta sanar da ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban taronta na kasa.

Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023
Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023 Hoto: APC
Asali: Facebook

Sai dai tsohon gwamnan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yanzu taron zai gudana mako daya kafin azumin Ramadana. Kuma idan shugaban kasa ya sanya hannu a sabon dokar zabe, hakan na nufin za a yi zaben fidda gwani tsakanin watan Yuni da Yli daidai da tanadin dokar zabe. Kun san sabuwar bukatar da ke dokar shine cewa a gudanar da zaben fidda gwani watanni shida kafin babban zabe.
“Daga abun da nake gani, jam’iyyar za ta shiga rudani saboda abun da suke son cimma shine gudanar da taron da zaben fidda gwani a rana guda don ganin fusatattun jiga-jigan jam’iyyar sun kasance cikin rashin mafita bayan taron.”

Wani tsohon gwamnan ya ce an jinkinta taron ne saboda gwamnan jihar Yobe na hararar kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

Ya ce:

“Duk ra’ayi ne kawai. Ya matsu yaga ya zama shugaban kasa nag aba ko kuma akalla mataimakin shugaban kasa.”

Rahoton ya kuma kawo cewa wata majiya ta ce wasu gwamnoni, musamman wadanda ke neman zango na biyu, suna kamun kafa da kwamitin riko don su ci bagas.

Burin Buni shine gyara APC ba wani abu ba – Hadiminsa

Da aka tuntube shi, kakakin Buni, Mamman Mohammed, ya yi watsi da ikirarin cewa ubangidan nasa na hararar kujerar shugaban kasa ne, inda ya bayyana hakan a matsayin hasashe daga tsoffin gwamnoni.

“An cika mu da wadannan zarge-zarge marasa tushe. Mai girma gwamna yana yin wannan aiki ne kawai don gyara jam’iyyar saboda yarda da shi da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NEC) ya yi. Bai taba tunanin ko tattaunawa da kowa cewa yana da sha'awar wani mukamin kasa ko na jam'iyya ba.
“Ku tuna, yana a zangonsa na farko ne a matsayin gwamna. Kawai dai hasashen wadanda suka makance da kudirinsu ne yasa basa ganin abubuwan alkhairin da gwamnan na jihar Yobe yake yiwa jam’iyyar. Da gangan muka ki kula wadanda ke yada jawaban karya kan gwamnan. Yana aiki ba jib a gani don gyara jam’iyyar kuma wannan shine aniyarsa. Duk wani abu bayan wannan hasashen masu fadinsa ne.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun bayyana goyon bayansu tare da amincewarsu da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyyar na kasa.

A jiya ne jam'iyyar mai mulki ta sanar da cewa ta kara wata daya cif a kan ranar zaben jam'iyyar da ta saka na kasa.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi ya sanar da hakan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ranar yau Talata a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel