Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun bayyana goyon bayansu tare da amincewarsu da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyyar na kasa.

A jiya ne jam'iyyar mai mulki ta sanar da cewa ta kara wata daya cif a kan ranar zaben jam'iyyar da ta saka na kasa.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi ya sanar da hakan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ranar yau Talata a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya
Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Gwamnonin sun samu ganawa a yammacin Litinin amma suka ki yin tsokaci kan dage gangamin zaben shugabannin jam'iyyar ga manema labarai.

"Har sai mun kammala ganawa da shugaban kasa, ba za mu iya tsokaci kan komai ba," shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyya mai mulki kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu yace.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari

Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari

A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ya shiga ganawar gaggawa da gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a dakin taron fadar Shugaban kasa Aso Villa, Abuja.

Wadanda ke hallare a ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni 18, rahoton DailyTrust.

Daga cikin gwamnonin akwai na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo, Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan Anambra.

Ana zaman ne bisa dage taron gangamin jam'iyyar da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayi wanda ya bar baya da kura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel