Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

  • Saura kusan mako daya ne rak ya rage a gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC a Najeriya
  • Kawo yanzu ba a san wanene shugaban kasa Muhammadu Buhari yake marawa baya a zaben ba
  • Hakan ya sa Gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki su ka rasa inda za su kama har yau

Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya rasa inda zai sa kansa a zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa wanda ake shirin yi nan da kusan mako guda.

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar a safiyar Juma’a, 18 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa duk da zaben ya karaso, ba a san inda aka sa gaba ba.

Jinkirin da shugaban kasa yake yi a game da babban zaben da za ayi ya sa gwamnonin jihohi, shugabannin rikon kwarya da ‘yan takarar APC a cikin duhu.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kejerar ministan mai, ta fadi dalili

Bangarori da-dama daga masu hangen shugaban kasa, gwamnoni, da wasu 'yan jam’iyya irinsu Yemi Osinbajo su na kokarin ganin na su ne ya samu mukami.

Shugaba Buhari ba ya nan

A halin yanzu shugaban Najeriya ya na kasar waje inda yake halartar taron EU-AU da ake yi. Wannan ya sa aka daga zaman da zai yi da gwamnonin APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin APC
Taron shugabannin APC Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Jaridar ta ce da zarar shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya, ana sa ran zai kira taro na musamman da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa.

Kan 'yan jam'iyya ya rabu

Kawunan gwamnonin APC ya rabu a game da zabin wanda zai zama shugaban jam’iyya na kasa. Hakan ne ta sa aka gagara barin takarar ga wani mutum daya.

Wata majiya ta ce idan shugaba Buhari ya dawo kasar, zai bayyana wanda yake goyon baya a zaben. Hakan zai sa APC ta samu shugaba ta hanyar maslaha.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

An kai takarar kujerar shugaban jam’iyya zuwa Arewa maso tsakiya ne, Amma akwai manyan ‘yan siyasar daga wani bangare da suke harin mukamin na APC.

Daga cikinsu akwai Abdulaziz Yari; Ali Modu Sheriff da Isa Yuguda da ba daga yankin suka fito ba.

Maganar da ake yi shi ne yanzu ana ganin Sanata Abdullahi Adamu ya fi karfi. Kwanaki kuwa maganar Al-Makura, Saliu Mustapha, da su Sani Musa ake yi.

Zaben 2023

Duk da bai ce zai yi takara ba, a makon nan ne aka ji wasu matukan Keke–Napep sun ce sai inda karfinsu ya kare wajen ganin Yemi Osinbajo ya karbi mulki.

Kungiyar TOAN ta ce ta na goyon Farfesa Osinbajo saboda kishin kasarsa, sanin aikin da ya yi da halayya, kwarjini, tsayin-daka, adalci da kuma kokarinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel