Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

  • Wani jami'in dan sanda ya bakunci lahira garin bude kofar gidan wani tsohon gwamna na jihar Ogun
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace kaddara ce daga Allah, za ta iya faruwa kan kowa
  • Sai dai, wani jami'in dan sandan da ya nemi a sakaya sunansa ya daura laifin kan tsohon gwamnan

Jihar Ogun - Wani dan sanda mai suna Sajan Adegoke Ogunsola ya mutu a gidan tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Dan sanda ya mutu a gidan tsohon gwamna
Karar kwana: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jami'in ya bayyana cewa Ogunsola ya kasance ma'abocin zama a gidan tsohon gwamna Daniel, wanda aka fi sani da Kotun Asoludero, a garin Sagamu a karamar hukumar Sagamu ta jihar.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Da yake bayyana lamarin da ya faru a ranar Asabar din da ta gabata, Oyeyemi ya bayyana mutuwar dan sandan a matsayin hadari da ka iya faruwa da kowa.

A cewarsa, dan sandan yana kokarin bude kofar gidan ne, inda cikin kuskure aka buge kansa, hakan ya zama sanadin mutuwarsa.

Kakakin rundunar ya ce an garzaya da sajan din zuwa asibiti amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Daniel yayi gwamnan jihar Ogun a tsakanin 2003 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

Laifin tsohon gwamnan ne, inji wani jami'i

Sai dai, wata majiyar ‘yan sanda da ta zanta da jaridar Premium Times ta daura laifin kan tsohon gwamnan, inda ta ce:

“Kowane VIP ana sa ran ya samu mai gadi, tun ma kafin a tura ‘yan sanda zuwa gidajensu domin ba da kariya.”

Kara karanta wannan

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

Wannan jami'i dai bai so a ambaci sunansa ba saboda shi ba kakakin rundunar ‘yan sanda ba ne.

Ya kara da cewa:

“Me ya sa dan sanda dauke da makami zai zama mai bude kofa? Me yasa 'yan siyasa za su mayar da 'yan sanda bayin su?
“Idan wani jami’i ya ki a yi amfani da shi a matsayin mai gadin a gidan, sai su kira DPO su ce ya canza shi a mayar da shi wani wurin aikin.
“Za a bukaci dan sandan da ke rike da makami ya bude kofa; direbobi, farar hula da kuma Daniel da kansa zai gaya wa jami'an su bude kofa. Idan da akwai mai gadi a gidan, wannan ba zai faru ba."

Najeriya ta yi rashi: Daya cikin wadanda suka rubuta taken Najeriya ya rasu

A wani labarin, daya daga cikin marubuta biyar na taken kasar Najeriya 'National Anthem' Farfesa Babatunde Ogunnaike ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu yana da shekaru 65.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

An haifi Ogunnaike a ranar 26 ga Maris, 1956 kuma ya fito ne daga garin Ijebu Igbo ta jihar Ogun.

Wani fitaccen masanin ilimi a Najeriya kuma mawallafi, Gbenro Adegbola ne ya tabbatar da mutuwarsa, inji rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel