Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara

Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara

  • Kotu ta yi watsi da bukatar hana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tsayawa takara a 2023
  • Kotu ta ce kungiyar da ta shigar da karar ba ta da yancin kalubalantar cancantar Atiku Abubakar din
  • A baya wata kungiyar ta shigar da kara kotu, ta bukaci alkali ya dakatar da Atiku Abubakar daga tsayawa takara

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, ta yi watsi da karar da ke kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na neman takarar kujerar shugaban kasa.

Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, Justis Inyang Ekwo, ya yi watsi da karar kan hujjar cewa bangaren da ya shigar da karar bai da yancin yin hakan.

Justis Ekwo ya bayyana mai karar a matsayin mai shiga sharo ba shanu, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara
Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ce wata kungiya, Incorporated Trustees of Elgalitarian Mission for Africa, a cikin wata kara mai lamba: FHC/ABaj/CS/177/2019 ta yi karar Atiku, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da Atoni Janar na tarayya.

Kungiyar ta EMA ta kalubalanci cancantar Atiku na yin takarar shugaban kasa kan hujjar cewa shi ba dan Najeriya bane.

Kungiyar ta nemi kotu ta riki cewa idan aka yi la’akari da sashi na 25(1)&(2) da 131(a) na kundin tsarin mulki da kuma lamuran da ke kewaye da haihuwar tsohon mataimakin Shugaban kasar, ba zai iya yin takarar babban kujera ba.

Jaridar Guardian ta kuma rahoto cewa gwamnatin jihar Adamawa da Atoni Janar dinta, ta nemi izinin kotu na shiga shari’ar a ranar 27 ga watan Yulin 2021.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

Kotun, a wata takarda mai kwanan wata 26 ga watan Afrilu wanda aka hada a ranar 24 ga watan Yuli, ta amince da rokon AG na Adamawa na neman a shigar da shi shari’ar a matsayin mutum na biyar.

Gwamnatin Adamawa ta sanar da kotu cewa Atiku ya cancanci neman kujerar shugaban kasa.

Ta ce Atiku, wanda aka shigar da karar a kansa, dan Najeriya ne kuma daga jihar Adamawa wanda aka zaba a matsayin Gwamnan jihar a 1999 kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin Shugaban kasar tsakanin 1999 zuwa 2007.

Ta bayyana cewa karar na barazana ga yancin dan Najeriya, dan asalin Adamawa da ke da kananan hukumomi 12 cikin 21 na jihar.

2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka

A baya mun kawo cewa ana daf da kawo karshen dambarwar da ake yi game da cancantar Atiku Abubakar na fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Cibiyar horar da lauyoyi ta kama da wuta, an zarce da mutum 5 asibiti

The News ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Adamawa, a ranar 27 ga watan Yuli, ta shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa Atiku Abubakar ya cancanta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

Legit.ng ta tattaro cewa attoni janar na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, yayin gabatarwa kotu hujojinsa ya shaidawa Mai Shari'a Inyang Ekwo cewa yana son a gwamutsa shari'ar da wata kungiya ta shigar kan Atiku da wasu mutum uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel