Karin bayani: Cibiyar horar da lauyoyi ta kama da wuta, an zarce da mutum 5 asibiti

Karin bayani: Cibiyar horar da lauyoyi ta kama da wuta, an zarce da mutum 5 asibiti

  • A daren Laraba 17 ga watan Faburairu ne dai harabar cibiyar horar da lauyoyi ta Najeriya ta kama wuta a jihar Legas
  • Majiyoyi sun yi ikirarin cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wata barakar da aka samu daga wutar lantarki a ranar Laraba
  • Ko da yake kusan nan take aka kashe gobarar, kimanin mutane biyar ne suka tsinci kansu a asibiti sakamakon afkuwar lamarin

Jihar Legas - An samu tashin gobara a daren ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu, a harabar cibiyar horar da lauyoyi ta Nigerian Law School dake kan titin Ozumba Mbadiwe a Victoria Island da ke jihar Legas.

Majiyoyin da suka zanta da ‘yan jarida sun bayyana cewa, lamarin ya haifar da tarzoma da tashin hankali a yankin.

Gobara ta yi barna a cibiyar horar da lauyoyi ta Legas
Da dumi-dumi: Cibiyar horar da lauyoyi ta kama da wuta, an zarce da mutum 5 asibiti | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, an nakalto daga majiya mai tushe a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu cewa gobarar ta tashi ne a sakamakon matsalar wutar lantarki da aka samu a cibiyar.

Kara karanta wannan

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Duk da haka, an kashe gobarar cikin kankanin lokaci.

Majiyar ta ce:

“An samu tashin gobara jiya da daddare, amma nan take aka shawo kan ta. Gobarar ta faru ne sakamakon lalacewar wutar lantarki."

A cewar rahoton daridar Vanguard, kimanin mutane biyar da gobarar ta shafa sun kwanta a asibiti a halin yanzu.

Rahoton ya ce:

“Gobarar ta zo da wani kara. An samu turmutsutsu a dakin kwanan dalibai. Na ga wani dalibin da ya yi tsalle daga bene na farko inda gobarar ta tashi kusa da dakin karatu. Wasu daliban sun fice daga dakunansu a firgice.
"Akalla, mutane biyar sun samu munanan raunuka yayin da wata tsohuwa mace mai aikin shara ta samu gurdewa a yatsar kafa."

Yadda Gobara ta kama kasuwar Nguru dake jihar Yobe ranar Asabar

Kara karanta wannan

Allah ya yi: Daga karshe dai an samo hanyar magance HIV, wata mata ta warke sarai

A wani labarin, shahrarriyar kasuwar karamar hukumar Nguru dake jihar Yobe ta kama da wuta da safiyar Asabar, 8 ga watan Junairu, 2022.

Wani mai idon shaida, Abubakar Ibn Usman, ya ce shaguna dauke da kayan miliyoyi sun kone kurmus.

Akalla shaguna 300 ne wannan mumunar gobarar ta shafa, riwayar TheCable. Shugaban kungiyar yan kasuwan, Ibrahim Adam, ya bayyana cewa gobarar ta fara ci ne misalin karfe 7 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel