2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka

2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da kotun tarayya da ke zamanta a Abuja cewa Atiku dan Nigeria ne
  • Afraimu Jingi, attoni janar na jihar Adamawa, ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 27 ga watan Yuli yayin da ya bayyana gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo
  • Wata kungiya, EMA ta garzaya kotun tana kallubalantar cancantar takarar shugabancin kasar da Atiku zai yi kan cewa ba a Nigeria aka haife shi ba

FCT, Abuja - Bisa ga dukkan alamu ana daf da kawo karshen dambarwar da ake yi game da cancantar Atiku Abubakar na fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023.

The News ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Adamawa, a ranar 27 ga watan Yuli, ta shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa Atiku Abubakar ya cancanta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa attoni janar na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, yayin gabatarwa kotu hujojinsa ya shaidawa Mai Shari'a Inyang Ekwo cewa yana son a gwamutsa shari'ar da wata kungiya ta shigar kan Atiku da wasu mutum uku.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

Kungiyar ta EMA cikin kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, ta yi karar Atiku, Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hukumar zabe mai zaman kanta, (INEC) da attoni janar na kasa, AGF, Abubakar Malami.

A cewar rahoto, EMA na kallubalantar cacantar Atiku na yin takarar shugaban kasa a kan cewa ba a Nigeria aka haife shi ba, rahoton Daily Trust.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba dan Nigeria bane ko Kamaru

The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba idan aka yi la'akari da sashi na 25(1) &(2) and 131(a) na kundin tsarin mulki da yanayin haihuwansa.

Amma Jingi, ta hannun lauyansa, Cif L.D. Nzadon, a kara mai dauke da kwanan watar ranar 26 ga watan Afrilu da aka shigar ranar 24 ga watan Yunin 2021 ya bukaci a gwamutse batutuwan wuri daya.

Lauyan ya bayyana lamarin a matsayin 'batu ne da mutanen kasa ke bibiya kuma ya dace a yi biyyaya a kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) a batun zaben shugaban kasar Nigeria.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

Nzadon ya ce Atiku, wanda aka shigar da karar saboda shi, dan kasa ne daga jihar Adamawa wanda aka zaba a matsayi gwamnan jihar a 1999 kuma ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Asali: Legit.ng

Online view pixel