Shugabancin ƙasa a 2023: Daga ƙarshe an bayyana inda Tinubu ya samo arzikinsa

Shugabancin ƙasa a 2023: Daga ƙarshe an bayyana inda Tinubu ya samo arzikinsa

  • Abdulmumin Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya kuma shugaban kungiyar masu goyon bayan Tinubu ya yi magana kan arzikin Tinubu
  • Jibrin ya bayyana cewa Tinubu yana da hannun jari a kamfanoni kamar Apple da kungiyar Manchester United sannan ya samu kudi wurin kasuwanci da kyauta da ake masa
  • Tun a kwanakin baya dama mutane da dama sun rika tambaya game da tushen arzikin na Tinubu suna zargin akwai yiwuwar ya tara kudin ba ta hallastaciyar hanya ba

Makonni bayan kin amsa tambaya game da inda Tinubu ya samo arzikinsa, Shugaban Kungiyar Masu Goyon Bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya yi wasu muhimman bayanai game da arzikin tsohon gwamnan na Legas.

A hirar da aka yi da shi a TVC News, an sake yi wa Jibrin, tsohon Dan Majalisar Wakilai tambaya game da inda Tinubu ke samun arzikin.

Kara karanta wannan

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa.

Shugabancin ƙasa a 2023: Daga ƙarshe an bayyana inda Tinubu ya samo arzikinsa
Abdulmumin Jibrin, Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu. Hoto: Tinubu Support Group -TSG, Abdulmumin Jibrin
Asali: Facebook

A martaninsa, Jibrin ya ce tun farko dama tushen arzikin Tinubu ba boyeyyen abu bane duba da cewa mutum ne da ya rike mukamai da dama a rayuwarsa.

A cewar tsohon dan majalisar, manyan kamfanoni na kasa da kasa sun dade suna neman Tinubu ya yi aiki da su tun lokacin yana makaranta, yana mai cewa tsohon gwamnan ya yi wa Mobil da wasu kamfanonin aiki kafin ya shiga siyasa.

Kalamansa:

"Ina tabbatar maka da cewa babu sanatan Najeriya da za a ce talaka ne kuma ya shiga siyasa ne a matsayinsa na Sanatan Najeriya.
"Yana da hannu da shuni ... wannan mutumin akwai kasuwanci a jininsa ... yana shigo da kaya daga kasashen waje, yana fitar da kayayyaki kuma mutanen da ke maganan sun san cewa ya dade yana daukan nauyin harkokin goyon bayan demokradiyya tun 1990s.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

"Don haka, Me yasa ba su tambayan inda ya samu wadannan kudin? Wannan mutumin yana da manyan hannayen zuba jari a duniya. Yana da hannun jari a kamfanin Apple. Apple da ka san cewa su kan yi bin didigi kafin su sayar wa mutum hannun jari.
"Ni kaina na yi mamaki a baya-bayan nan a lokacin da na ke kallon kwallo tare da shi ... na gano cewa yana da hannun jari a Manchester United. Don haka ya dade yana kasuwanci. Ko da ka ajiye wannan a gefe, idan ka duba girmansa da matsayin da ya kai a siyasa, ba Najeriya kadai ba har a duniya, ya kamata ka san cewa shi ba karamin mutum bane.
"Don haka za ka iya kasa arzikinsa kashi biyu, na farko daga kasuwancinsa, ayyukan da ya yi a rayuwarsa sannan kashi na biyu alherin da ya ke samu daga masoyansa da abokan arziki, kuma hakan bai kamata a yi mamaki ba."

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Ba a taba tantama game da cancantar Tinubu ba

Jibrin ya cigaba da cewa, dama ba a taba tantama game da cancantar Tinubu ba, yana mai cewa ana iya ganin ayyukan da ya yi a wuraren da ya yi aiki.

Ya ce jagoran na APC ya yi hakan a Legas, yana mai cewa tsare-tsaren da ya yi a Legas suna amfanar Najeriya har yanzu.

Da ya ke magana game da shekarun Tinubu, Jibrin ya ce abin kunya ne yan jarida su rika tambaya game da shekarunsa duba da cewa ya kan yi bikin zagayowar shekarunsa a kowanne shekara, ya ce shekarun Tinubu 69 zai shiga 70

Asali: Legit.ng

Online view pixel