Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

  • 'Yan Najeriya sun shiga mawuyacin hali yayin da ake fama da karancin man fetur a wasu sassan kasar nan
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya ke koka tsadar abinci a kasar, tare da hauhawar farashi
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi martani, inda suka bayyana irin kokensu game da wannan mummunan yanayi

‘Yan Najeriya sun tafi shafukan sada zumunta domin nuna damuwa, bacin rai da kuma fusata kan karancin man fetur da ke kara ci gaba da dabaibaye wasu sassan kasar nan.

An ga dogayen layukan da aka yi a safiyar yau a wasu sassan Legas da Abuja, lamarin da ya sa masu ababen hawa kokawa da hawan farashin mai a daidai lokacin da matsalar karancin abinci ke kara kamari.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Layin man fetur ya jawo cece-kuce a Abuja da Legas
Mun shiga uku: 'Yan Najeriya sun hasala, sun fara kokawa kan karancin man fetur | Hoto: vanguardngr.com

Wani mashahurin Fasto @Olubankoleidowu, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Mun shiga uku! Wannan sabon karancin man fetur yana tunatar da mu wace shawara ya kamata mu yanke a 2023. ’yan Najeriya ku bi a hankali. Allah ba zai sauko daga sama domin ya muku yaki ba, shi ya sa ya ba ku kwakwalwa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin 'yan soshiyal midiya

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Alex Ekubo, na daya daga cikin ‘yan Najeriya da dama da suka nuna alhininsu dangane da karancin man fetur a kasar.

Ya rubuta:

“Rashin tabbas a wannan Najeriyar yana da ban tsoro. Ka fita kawai ka dawo, bum! Karancin mai.”

@salihusakpe ya ce:

"Wannan ita ce Najeriya inda za ta yi fari yanzu sannan minti na gaba ta koma baki."

Wani dan Najeriya, @iamangelraf: ya yi mamakin dalilin da ya sa za a ke samun karancin man fetur, ya ce:

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

"Za ka kara tsanar Legas duk lokacin da ake fama da karancin mai.
"Bayan sayen data, man fetur ke gaba. Da kyar 'yan Najeriya za su iya rayuwa ba tare da wadannan kayayyakin ba."

@tesla_tunes ya ce:

"Kada su raina mana hankali mana, wane abu ne kuma karancin mai a wannan lokacin. Ba wannan lokacin ba pls"

@solaceomolaiye ya rubuta:

"Yawan layi a Abuja yana kara ta'azzara saboda karancin PMS, kamar muna da bakin haure daga Legas zuwa Abuja."

Wata majiya da ta so a sakaya sunanta, ta yi ikirarin cewa wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama da shi na karancin man fetur ya samo asali ne sakamakon karancin man fetur a gidajen man.

Hakazalika, majiyar ta yi watsi da rade-radin cewa cire tallafin man na da nasaba da karancin man da ake fama da shi a yanzu, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

A wani labarin, ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce.

NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel