Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa

  • Bayan kwanaki goma a garkame, Lauyoyin tsohon kwamishanan Ganduje sun nemi a sassauta sharrudan beli
  • Alkali ya bayar da sharruda uku da ya wajaba Muaz Magaji ya cika kafin a sakesa daga gidan gyaran hali
  • Gwamna Ganduje ne ya shigar da karar Muaz Magaji kotu bisa zargin batancin da yayi masa a yanar gizo

Kano - Lauyoyin tsohon kwamishanan ayyukan jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji, sun bukaci kotu ta sassauta sharrudan karban belin da aka sanya masa saboda sunyi tsauri.

Mun kawo muku a baya cewa wata kotu da ke zamanta a unguwar Nomansland ta bayar da belin ne kan naira miliyan daya da wasu sharuda.

Sharrudan sun hada wanda ya hada kawo mutane biyu da zasu tsaya masa. Mutum daya ya kasance Limamin unguwar garinsa ko kwamdanda Hizbah, na biyu kuma Dagacin kauyensa da jingine fasfot dinsa.

Kara karanta wannan

Tarihi a 2022: Manya-manyan laifukan kashe-kashen tsafi 4 da suka girgiza 'yan Najeriya

Jagoran Win/Win Mu'az Magaj
Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa Hoto: DailyNigerian
Asali: Twitter

Freedom Rediyo ta ruwaito lauyoyin da cewa tun ranar da aka bada belin Dan Sarauniya suka dukufa cika sharrudan don a samu ya fito daga kurkuku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar rahoton, Lauyoyin sun ce tun a ranar Dagaci da Limamin garinsu Muaz Magaji suka hallara suka cika Fom din karban belinsa.

Hakazalika an jingine fasfot din tafiye-tafiyensa bayan kawota daga Abuja.

Menene matsalan?

Lauyoyin sun bayyana cewa sun yiwa sharadin da Alkali ya bada na Limani gurguwar fahimta.

A cewarsu,

"Washegari Talata mun samu ganawa da Alkali wanda ya fayyace masa ai ba Limanin garinsu Dan Sarauniya ake nufi ba, limamin garin Dawakin Tofa ake bukata."
"A nan muka fahimci cewa mu da magatakardan kotu mun yiwa sharrudan kotun kuskuren fahimta."

Lauyoyin sun cigaba da cewa wannan sharadi na kawo limamin Dawakin Tofa da kamar wuya saboda Limamin na daukan umurni ne daga wajen Hakimin Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Shi kuma Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Isma'il Umar Ganduje, dan'uwa ne ga wanda ya shigar da kara, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kama Muaz Magaji

Ana zargin Muaz Magaji da wallafa hoto na ɓata suna a dandalin sada zumunta.

Yan sanda sun gayyaci tsohon Kwamishinan bayan karar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shigar kansa.

Yan sanda sun tabbatar da kama shi ta bakin kakakin yan sanda Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce an shigar da korafi a kansa ne.

Ya ce rashin amsa gayyatar da suka dade suna yi wa tsohon Kwamishinan yasa aka kama shi.

Gwamna Ganduje ya yi korafi game wallafa hotunan bata sunansa da Magaji ya yi

A cikin takardar korafin da gwamnan ya aike, an shaida wa kotu cewa Magaji ya wallafa wani hoto da ke nuna wanda muke karewa (Ganduje) a matsayin mutum mara tarbiyya da tsohon Allah da ke aikata baɗala da wata mata wanda aka haska fuskar ta a hoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel