Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

  • Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya kawo tsarin makarantun Almajirai
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya kafa wadannan makarantu na zamani a jihohin Arewacin kasar nan
  • Jonathan ya ce ya yi wannan yunkuri ne domin ganin Almajirai sun hada da karatun ilmin zamani

Bayelsa – Goodluck Ebele Jonathan ya ce gwamnatinsa ta kawo wannan shiri ne domin ganin an cusa ilimin zamani a cikin manhajar karatun musulunci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto tsohon shugaban kasar yana cewa sun yi hakan ne da nufin daliban su samu aiki, sannan kuma a magance matsalar rashin tsaro.

Dr. Jonathan ya bayyana wannan a ranar Litinin, 7 ga watan Fubrairu 2022, yayin da yake jawabi a wajen wani taro a kan ilmi da aka shirya a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

An yi wa taron da aka yi garin Yenagoa, Bayelsa take ne da: ‘Optimizing the Delivery, Performance and Sustainability of Outcomes in the Education Sector.’

Ina abin ya dauko asali?

“A lokacin ina mataimakin shugaban kasa, ina magana da wani daga cikin masu ba ni shawara (mutumin Anambra) kan matsalar Arewa da yadda za a magance ta.”
“Wasu daga cikin gungun yaran nan ba su da kyakkayawar makoma, bai kamata mu bari a cigaba da tafiya a haka ba, saboda gudun a samu wata matsala a nan gaba.”
Almajirai a Arewa
Wasu Almajirai a Najeriya Hoto: Almajiri Is Also A Child, @4almajiri
Asali: Facebook
“Mu ka zagaya Arewa, mu ka yi magana da malaman da ke koyar da yaran nan a karkashin bishiya da cikin kango, mu ka yi zama da Sarakuna da dai sauransu.”

- Goodluck Jonathan

Kara karanta wannan

Gwamnoni, Sanatoci, tsofaffin masu mulki 100 sun hadu domin ceto Najeriya kafin zaben baɗi

The Guardian ta ce tsohon shugaban ya ce sun yi kokarin tattaro wadannan Almajirai wadanda suka ba Kur’ani muhimmanci, aka ga bukatar a gyara tsarin karatunsu.

Goodluck Jonathan: Almajirai na da ilmi

“Wasu daga cikinsu za su iya haddace Al-Kur’ani, duk wanda ya haddace littafi mai tarin yawa irin wannan, karya ne ka ce wannan mutumi bai da ilmi."
“Su Almajiran nan su na ganin su na da ilmi, amma al’umma ba ta karbe su ba. Ko a matakin kananan hukumomi, gwamnati ba ta ba su ko da aikin masinja.”

Jonathan ya ce dalili kuwa shi ne babu ilmin zamani a cikin tsarin karatun Al-Kur’anin na su. Don haka gwamnatinsa ta ce dole a taimaka masu, a shigo da su gari.

“Ba za a cire komai daga tsarinsu ba, amma za su hada da wasu bangaren ilmin zamani ta yadda idan sun kammala, za su iya karanta likitanci ko injiniyanci.”

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

- Goodluck Jonathan

Ta'adin 'yan bindiga

A makon nan ne aka ji wani labari maras dadi cewa ‘Yan bindiga sun kashe Bayin Allah a jihar Zamfara, kuma sun hana ‘Yan gari su yi masu jana’iza har yanzu.

Mutanen kauyen Daraga a karamar hukumar Maru su na kokawa a game da halin rashin tsaron da suke ciki, baya ga kashe masu mutaen 12 da aka yi kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel