Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya samu goyon bayan wata kungiyar kudu maso gabas kan aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Kungiyar mai suna Atiku Kawai ta bayyana cewar dan siyasar ne kadai zai iya magance matsalolin da ke addabar kasar
  • Ta bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan Inyamurai da sauransu kan bukatar zabar Atiku a jihar Enugu

Enugu - Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, kungiyar Atiku Kawai reshen kudu maso gabas, ta ce tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ne zai iya kawo mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a taron ta da ya gudana a Enugu yayin da take wayarwa Inyamurai da sauransu kai kan bukatar marawa Atiku baya a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai
Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

A wata sanarwa da daraktan kungiyar, NwaJesu Anthony Onyekuru, ya fitar, kungiyar ta ce lokaci ya yi da za a ceto kasar da daura ta a kan turban ci gaba, jaridar Guardian ta rahoto.

Sanarwar ta ce:

“Mun yarda cewa Atiku zai iya magance matsalolin da suka addabe mu a matsayinmu na mutane da kasa. Abun da kuke gani a yau gwaji ne na abun da zai zo, saboda mun shirya tsaf.”

Jaridar The Sun ta nakalto jagoran taron, Okezie Amujiogu, yana cewa:

“Mun zo nan ne domin nuna cewa a shirye muke mu marawa Atiku baya a babban zaben 2023 kuma za mu tara mutanenmu a kudu maso gabas don shugabancinsa.”

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

A wani labarin, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalong ya yi hannunka mai sanda ga tsofaffin yan siyasar da ke neman shugabancin kasar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Dalong ya ce kamata yayi duk dan siyasar da ya haura shekaru 65 ya duba yiwuwar zuwa majalisar dattawa sannan ya hakura da kudirin yin takarar kujerar shugaban kasa, Sahara Reporters ta rahoto.

Tsohon ministan shugaban kasa Muhammadu Buharin, ya jadadda cewar a yanzu Najeriya na bukatar mutum mai ji da karfi a matsayin shugaban kasa maimakon tsoffin mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel