Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

  • Gabanin zaben 2023, Tinubu na ci gaba da tuntubar jiga-jigai kan fatansa na zama shugaba a Najeriya a zaben 2023
  • Sai dai wasu masu goyon bayan Tinubu, sun yi kira ga mataimakin shugaban kasa Osinbajo da ya mika goyon bayansa ga Tinubu, kasancewarsa jagoran APC
  • A halin da ake ciki, tun da farko Osinbajo ya ja kunnen magoya bayansa kan kalaman batanci ga shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa

An bukaci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa tare da yin gangami wajen ganin Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023.

Wani shugaban matasa a yankin Neja Delta, Mista John Dekawei ne ya yi wannan kira a Warri yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce ya kamata Farfesa Osibanjo ya kasance mai biyayya ga jagoran siyasarsa, wato Tinubu ta hanyar mara wa takararsa ta shugaban kasa baya, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Lissafin Tinubu zai canza, Osinbajo yana daf da tsayawa takarar shugaban kasa

Tinubu da Osinbajo batun tsayawa takarar 2023
Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan kudu sun nemi Osinbajo ya dakata batun neman gadon Buhari | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Farfesa yemi Osinbajo bai kamata ya manta da rawar da Tinubu ya taka na tabbatar da ya zama mataimakin shugaban Najeriya ba. Daidai ne ga wani mutum ya kasance mai saka alheri ga mai taimakon sa.
"'Yan Neja Delta ba za su bata lokaci ba wajen kada kuri'unsu ga Tinubu a zaben 2023, Jagaban ne kadai mafita ga kawo ci gaba a Najeriya da Neja Delta.
"A shirye nake na tara mutane masu ma'ana don nuna goyon baya ga Tinubu a Neja Delta. goyon bayan Tinubu goyon bayan dimokradiyya ne da ci gaban Nigeria da kuma Neja Delta."

Lokacin da Osinbajo zai bayyana kudurin gaje kujerar Buhari

Wasu majiyoyi na kusa da tawagar yakin neman zaben mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sun bayyana cewa zai bayyana yiwuwar tsaya takararsa ta shugaban kasa bayan taron gangamin APC na kasa.

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

Majiyar ta ce duk da yunkurin 'yan yankin Kudu maso Yamma na hana Osinbajo tsayawa takara, ya yanke shawarar shiga jerin 'yan takarar kuma mai yiyuwa ne ya zama magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Har ila yau, daya daga cikin majiyoyin da suka zanta da jaridar This Day a kwanakin baya ta bayyana cewa a mafi yawan sassan kasar nan da Osinbajo ya kai ziyara, kiran da ake yi shi ne ya tsaya takarar shugaban kasa.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa.

Bello, ya sanar wa masoyansa dake faɗin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel