Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

  • Tsohon ministan Buhari, Solomon Dalong ya shawarci yan siyasar da suka haura shekaru 65 da su hakura da neman kujerar shugabancin kasa
  • Dalong ya ce kamata yayi su mayar da hankali wajen zama sanatoci a majalisar dokokin tarayya
  • Ya ce matasa masu jini a jika ne ya kamata su dare kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023

Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalong ya yi hannunka mai sanda ga tsofaffin yan siyasar da ke neman shugabancin kasar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Dalong ya ce kamata yayi duk dan siyasar da ya haura shekaru 65 ya duba yiwuwar zuwa majalisar dattawa sannan ya hakura da kudirin yin takarar kujerar shugaban kasa, Sahara Reporters ta rahoto.

Tsohon ministan shugaban kasa Muhammadu Buharin, ya jadadda cewar a yanzu Najeriya na bukatar mutum mai ji da karfi a matsayin shugaban kasa maimakon tsoffin mutane.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da suka san a raba jiha da Buhari, Saraki ya fasa kwai

Ku tafi majalisar dattawa, ku bar matasa su nemi shugabancin kasar – Tsohon minista ga Atiku, Tinubu
Ku tafi majalisar dattawa, ku bar matasa su nemi shugabancin kasar – Tsohon minista ga Atiku, Tinubu Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya raka shugaban kamfanin King Adebayo Film and Theatre Arts Network Television, Prince Adewole Adebayo, wanda ya ayyana aniyarsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 a Abuja, Daily Post ta rahoto.

Dalong ya ce:

“Na yarda cewa yakamata duk mutanen da suka kai shekaru 65 zuwa sama su mayar da karfinsu wajen zama sanatoci maimakon yin takarar shugabancin kasa.
“Ya zama dole su barwa matasa kujerun shugabanci. Mun murkushe makomarsu tun 1999 kuma ba mu yi nasarar gina musu makoma ba.
“Don haka, ya kamata mu janye sannan mu barsu don gobensu. Idan suka yi nasara, sai suyi murna sannan idan suka gaza, kansu za su tuhuma.
“Bana son wannan wasar mara karewa na tsara makomar matasa. Don haka bama so duk wanda ya kai shekara 65 ya nemi shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

“Ofishin na bukatar abubuwa da dama, yana bukatar kuzari sosai kuma bama son wani ya je wajen ya zama mai taushi da mika ayyukansa ga wadanda ba zai iya sanyawa ido ba saboda shekaru.”

Ana ganin sakon kai tsaye ne ga wasu shahararrun yan takara wadanda ke da ra’ayin darewa kujerar kamar babban jigon APC na kasa, Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Yayinda shekarun Atiku Abubakar ya kasance 75 a yanzu, Tinubu ya doshi shekaru 70 a duniya.

Osinbajo ya magantu kan yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya karyata rahotannin cewa yana shirin ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa bayan babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022.

Babban mai ba mataimakin shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin labarai, Laolu Akande, ya ce rahoton karya ne kuma hasashe kawai ake yi.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Akande ya kara da cewar duk wani bayani kan hukuncin mataimakin shugaban kasar zai fito ne kai tsaye daga ofishinsa amma ba wai daga yan jarida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel