Da dumi-dumi: Osinbajo ya magantu kan yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023

Da dumi-dumi: Osinbajo ya magantu kan yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya magantu a kan zargin shirinsa na ayyana neman takarar shugaban kasa
  • Osinbajo ya ce rahotannin da ke yawo cewa zai kaddamar da shirinsa na neman kujerar Buhari bayan babban taron APC ba gaskiya bane
  • Hadimin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya ce duk wani shiri na ubangidan nasa zai fito ne kai tsaye daga ofishinsa amma ba wai a kafofin labarai ba

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya karyata rahotannin cewa yana shirin ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa bayan babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022.

Babban mai ba mataimakin shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin labarai, Laolu Akande, ya ce rahoton karya ne kuma hasashe kawai ake yi.

Kara karanta wannan

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Da dumi-dumi: Osinbajo ya magantu a kan zargin shirinsa na ayyana neman takarar shugaban kasa
Da dumi-dumi: Osinbajo ya magantu a kan zargin shirinsa na ayyana neman takarar shugaban kasa Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Akande ya kara da cewar duk wani bayani kan hukuncin mataimakin shugaban kasar zai fito ne kai tsaye daga ofishinsa amma ba wai daga yan jarida ba.

Hadimin mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a daren ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta:

“Na ga labarai cewa mataimakin shugaban kasa zai sanar da aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa bayan taron APC. Duk wanda ke karanta labarin zai san cewa duk karya ne da hasashe.
“Duk bayanai kan harkoki da hukuncin mataimakin shugaban kasa zai fito kai tsaye daga ofishinsa amma ba wai rade-radi da ake daukar nauyi a kafofin watsa labarai ba.”

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Kara karanta wannan

Lissafin Tinubu zai canza, Osinbajo yana daf da tsayawa takarar shugaban kasa

A wani labarin, an bukaci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa tare da yin gangami wajen ganin Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023.

Wani shugaban matasa a yankin Neja Delta, Mista John Dekawei ne ya yi wannan kira a Warri yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce ya kamata Farfesa Osibanjo ya kasance mai biyayya ga jagoran siyasarsa, wato Tinubu ta hanyar mara wa takararsa ta shugaban kasa baya, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel