2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

  • Mai neman kujeran shugaban kasa a zaben 2023 ya bayyana babbar manufarsa idan ya samu nasara
  • Mutumin yace da yan mata masu amfani da jikinsu wajen samun kudi zai fara na shi aikin
  • A cewarsa, da yawa daga cikinsu talauci ke jefasu harkar, saboda haka zai wayar musu da kai

Bauchi - Wani mai niyyar takara a zaben shugaban kasa a 2023, Mista Tanimu Audu, ya yi alkawarin kawar da karuwanci inda har yan Najeriya sun zabeshi ya zama shugaba.

Audu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Laraba jihar Bauchi, rahoton TheSun.

Ya bayyana cewa babban dalilin da ke jefa yan mata harkar karuwanci shine rashin aikin yi kuma gwamnati bata sama masu yadda zasu yi da rayuwarsu ba.

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Yace:

"Idan aka zabe ni, gwamnati na za ta haramta karuwanci ta hanyar tarbiyyantar da yaran dake suka dauki mumunan aikin a matsayin sana'a."
"Yawancinsu sun tsinci kansu cikin wannan harka ne saboda bakin talauci da wahala."

2023: Zan kawar da karuwai
2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Ya yi alkawarin cewa kawar da karuwanci na daya daga cikin manyan manufofinsa idan ya zama shugaban kasa.

Sauran abubuwan da yayi alkawarin magancewa sune fashi da makami, garkuwa da mutane, dss.

Ya kara da cewa za'a baiwa duk matashin da ya kammala karatun digiri bashin kudi jari ba tare kudin ruwa ba.

Tsohon sanata, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

Ayyanawar tasa na zuwa ne bayan tsohon jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, Dan Majalisar Dattawa, Orji Kalu, da tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha, suka bayyana tasu aniyar.

Saraki, tsohon Gwamnan Kwara ya ce yana da kyakkyawan tarihi na gudanarwa da gogewa wajen tafiyar da lamurra yadda ake bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel