Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

  • Wata kungiyar siyasa ta Fulani ta fito ta marawa Tinubu baya kan kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
  • Sun bayyana hujjojinsu da cewa, Tinubu ya cancanci takarar saboda alakarsa mai kyau da Fulani a kasar
  • Hakazalika, kungiyar ta ce Tinubu ne dan takarar da zai iya hada kan 'yan Najeriya domin a samu maslaha

FCT, Abuja - Daily Trust ta rahoto cewa, wata Kungiya mai suna Fulani Political Forum, ta shiga jerin magoya bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu a yakin neman tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Shugaban kungiyar, Alhaji Ya’u Haruna, ya bayyana goyon bayansu ga Tinubu a wani taron kasa da ya samu halartar shugabannin NPF daga sassan kasar a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Bola Tinubu fulani suka zaba
Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Alhaji Ya’u, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal-Hure (Arewa maso Yamma) ne na kasa, ya bayyana cewa kungiyar ta amince da Tinubu ne saboda damuwarsa kan halin da Fulani ke ciki.

Ya kuma yi nuni da cewa, Tinubu ne ya shiga tsakani don warware rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a Benue.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Ta haka, Tinubu ya nuna cewa shi dan Najeriya ne na gaskiya kuma shugaba mai sanin ya kamata wanda zai kawo karshen rikici da wahalhalun da Fulani ke fuskanta a halin yanzu."

Ya yi nuni da cewa, duk da kasancewar mambobin wannan dandalin suna da jama’a a sassan kungiyoyin al’adun Fulani da ba su da alaka da siyasa, amma sun taru a matsayin kungiya daya domin zabar ‘yan takara da za su kawo maslaha ga Fulani.

Kara karanta wannan

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun a 1997

Daily Trust ta ce ‘ya ‘yan jam’iyyar na APC mai mulki su na so Bola Tinubu ya janye wasu kalamai da ya yi a shekarun baya kafin ya san zai nemi shugabanci.

Tun da yanzu ya na da niyyar neman takarar shugaban kasa, magoya bayan na APC sun nemi Tinubu ya janye kalaman da ya yi kan rashin imani da Najeriya.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos, jihar Filato, Saleh Mandung Zazzaga ya ce kalaman na Tinubu za su iya jefa shi da jam’iyyarsu duk a cikin matsala.

A cewar Salhe:

“A wata hira da aka yi da Bola Tinubu wanda ta fito a ranar 13 ga watan Afrilu, 1997, an rahoto shi yana cewa ‘ban yarda Najeriya kasa-daya ba’.”

A wani labarin, rahotanni sun bayyana a game da yadda yunkurin shigo da Dr. Goodluck Jonathan, da ba shi takara cikin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa ya ruguje.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a makon da ya wuce inda ta bayyana cewa kokarin da wasu ke yi na zawarcin Jonathan zai iya kawowa Rotimi Amaechi cikas.

Rahoton na Saturday Vanguard ya nuna cewa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN da wasu na kusa da shi ne suka yi ta zawarcin shugaba Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel