Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su ji tsoron shugabancin dan Ibo a zaben 2023
  • Umahi ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yi na cewar idan har dan kabilar Ibo ya zama shugaban kasa, yana iya raba kasar
  • Ya ce mutanen yankin kudu maso gabas sun zuba hannun jari a fadin kasar don haka babu yadda za a yi mutum ya cinnawa gidansa wuta

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bukaci 'yan Najeriya da kada su ji tsoron shugabancin kabilar Ibo a zaben 2023 mai zuwa.

Umahi ya yi wannan kira ne a Abakaliki, babbar birnin jihar a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, yayin wata liyafa da aka shirya masa bayan ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a makon nan, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba
Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa duk dan kudu maso gabas da ya zama shugaban kasa na iya raba kasar, Channels TV ta rahoto.

Ya kara da cewa ‘yan kabilar Ibo sun zuba jari a ko’ina a fadin kasar, yana mai cewa ba abu ne mai yiwuwa ba a yi tunanin ballewa a lokacin da suke mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umahi ya ce:

"Wasu makiyan kudu maso gabas sun ce idan muka zama shugaban kasa za mu raba kasar; ta yaya za mu raba kasar alhalin mun zuba jari a ko'ina?"

Da yake magana game da fafutukar neman yankin Biyafara, Umahi ya ce jihar Ebonyi ba za ta shiga fafutukar ba.

Ya kara da cewa:

“Da farko dai, na dade ina fadi, idan wani ya fada muku batun Biyafara, ku fada musu jihar Ebonyi ba za ta taba kasancewa cikin kasar Biyafara ba. Mu ba Biyafara bane.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

“An zalunce mu sosai kuma yanzu muna neman kafafunmu kuna son mu koma baya? Ba za mu koma ba. Ba za mu koma ba."

A cewarsa, Ebonyi ta fi kyau a Najeriya saboda jihar na da hannun jari a ko’ina kuma mutum ba zai iya cinna wa gidansa wuta ba.

Ya sha alwashin cewa idan ya zama shugaban kasa, zai ci gaba da ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma zai yaki cin hanci da rashawa a Najeriya.

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

A wani labarin, Shahararren dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya ce Allah ne ya tanade shi domin ya zama shugaban kasar Najeriya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Momodu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, yayin wata hira da Channels TV.

Dan siyasar dai ya bayyana aniyarsa ta takarar Shugaban kasa lokacin da ya gana da Ayirchia Ayu, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel