Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa a shirye yake yayi takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar APC da kowa ciki kuwa harda babban jigon jam'iyyar, Bola Tinubu
  • Kalu ya ce yana da duk abun da ake bukata daga mutumin da zai dare kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a 2023
  • Ya kuma ce takarar Tinubu ba zai taba zama matsala ga fitowar dan Ibo a matsayin shugaban Najeriya ba

Bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce a shirye yake ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da jigon jam'iyyar na kasa, Bola Tinubu, idan aka mika shi yankin kudu.

Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata
Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce ya yarda cewa zagayen kudu maso gabas ne samar da shugaban kasa na gaba, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Da aka tambaye shi kan ko yana kallon kudirin Tinubu a matsayin cin amanar Ibo, Kalu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bana son yin magana kan kudirinsa. Abun da na sani shine cewa muddin jam’iyyar ta mika tikitinta ga kudu, kudu maso gabas ya kamata a fifita sama da duk wani da ke neman tsayawa takara.
"Haka ya kamata ya kasance kuma shine abun da na dogara da shi. Zan shirya tsaf don fuskantarsa a Eagle Square kuma zan same shi."

A ruwayar Punch, ta ce da aka tambayi kan abun da ayyana kudirin shugabancin Tinubu ke nufi ga takarar dan Ibo a 2023, Kalu ya ce:

"Bana kallon takarar Tinubu a matsayin wata matsala ga fitowar shugaban Najeriya daga yankin Ibo. Baya da wani tasiri.
"Muna magana kan abun da yakamata Najeriya ta kasance. Muna magana ne kan abun da yakamata mutane su yarda shi. Obasanjo ya yi shugaban kasa tsawon shekaru takwas. Osinbajo zai yi shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa, kuma tun bayan samun yancin kai babu dan Ibo da aka zaba a matsayin shugaban kasa bisa tafarkin damokradiyya. Don haka yana da kyau ayi tunanin abun da ya kamata da kuma abun da zai fi yin kasuwa. Wannan abun tamkar matacce ne daga zuwa. Ba zai yi aiki ba.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

"Ni ne dan takarar shugaban kasa da ya fi kowanne shiryawa a Najeriya. Zan iya ta bangaren lafiya, zan iya a matsayina na mutum, zan iya da aljihu na. Zan iya fuskantar kowa. Amma jam'iyyar ita ce koli. Kawai ina jiran APC ne a matsayinta na jam'iyya.
"A gare ni, takarar shugaban kasa ba shine matsala ba. Matsalar shine wanda zai jagoranci kasar zuwa ga tafarkin tattalin arziki mai ban al'ajabi, da kawo sauyi. Bana adawa da Tinubu. Idan aka mika shi yankinsa kuma jam'iyyar ta nemi ya tafi. Don haka, jam'iyya ita ce koli. Kawai ina jiran jam'iyyar ne.
"Don takarar shugabancin kasar, Ina ganin na shirya sosai. Na yi shi a baya a 2007 kuma idan aka duba yiwuwar takara, zan zama mafi cancanta. Ina da duk abin da ake bukata don fuskantar kowane dan takara."

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

A baya mun kawo cewa, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya bayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa.

Kalu ya ce zai duba yiwuwar yin takarar ne idan har jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mika tikinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel