Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

  • Mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, dai ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Momodu ya ce Allah ne ya tanade shi domin ya gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe na gaba
  • Dan jaridar ya kuma ce zai iya karawa da manyan yan takarar jam'iyyar irin su Atiku Abubakar da sauransu domin yana da magoya baya sosai

Abuja - Shahararren dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya ce Allah ne ya tanade shi domin ya zama shugaban kasar Najeriya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Momodu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, yayin wata hira da Channels TV.

Dan siyasar dai ya bayyana aniyarsa ta takarar Shugaban kasa lokacin da ya gana da Ayirchia Ayu, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023
Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023 Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Mawallafin ya yi takara a zaben shugaban kasa na 2011 karkashin jam’iyyar National Conscience Party (NCP).

Da aka tambaye shi ko zai iya karawa da Atiku Abubakar da sauran yan takarar PDP, Momodu ya ce shine babban dan takara a Najeriya, inda ya kara da cewar babu dan takarar da ke da abokai a wajen jam’iyya kamar shi.

Ya ce yana da magoya baya sosai a tsakanin matasa, wanda ya bayyana a matsayin jam’iyyar siyasa mafi girma, inda yace jam’iyyarsa na bukatar dan takarar da ke dasawa da matasa don kayar da APC.

Ya ce:

“Bana son furucina ya zama mara dadi. Babu wani da ya fi karfin Dele Momodu a Najeriya. Ba wai Ina maganar jam’iyya bane ma.
“Zan kasance daya daga cikin tsirarun yan takara da ke da kamanceceniya da Cif Abiola wanda zai samu goyon baya a wajen jam’iyya. Babu wani mutum da ke dogaro da jam’iyyarsa kadai da zai kasance hankali kwance don cin zabe. Ina daya daga cikin yan kadan din.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

“Da na shigo PDP, aikin farko da na fara shine neman matasa su fara rijista a yanar gizo -iampdp.com - Ku je ku duba yawan mutanen da suka yi rijista.
“Idan ba za ka iya motsa matasa, jam’iyyar siyasa mafi girma- matasa - ina kiransu jam’iyyar masu zabe, idan jam’iyya ta yi watsi da masu zabe sannan ka ce za ka kayar da jam’iyya mai mulki kamar APC, inda suke da mutanen da basu damu da komai ba.
“Dole a samu dan takara mai nagartaccen tarihi, babu badakala. Dole a samu dan takara na matasa. Dole a samu dan takara wanda ke da duniya.
“Dole a nemi dan takara wanda ke shiri da kowa amma mai tsayin daka wanda zai iya fadin gaskiya ga masu mulki. Ina ta fadin gaskiya ga masu madafun iko duk da cewar mafi yawansu abokaina ne. Da wuya ka samu irin wannan a kowace jam’iyyar siyasa. Allah ne ya kebe Dele Momodu saboda wannan matsayin.”

Kara karanta wannan

2023: Ubangiji ne yace in fito takara, bai bani tabbacin zan ci ba, Gov Dave Umahi

Da aka tambaye shi kan ko zai bar PDP idan bai samu tikiti ba, ya ce zai marawa duk dan takarar da ya zama zabin jam’iyyar.

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

A baya mun kawo cewa, Dele Momodu, a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, ya je sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Labari ya iso Legit.ng Momodu ya gana da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiorchia Ayu, domin bayyana burinsa ga jam’iyyar.

Sanye da babbar riga da hula, Momodu ya mika takardar neman tsayawa takarar shugaban kasa ga shugaban jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel