Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da zai sa ba za a ba Kudu damar takarar shugaban kasa a 2023 ba
  • Ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 9 ga watan Janairun 2022
  • Hakazalika, Kwankwaso ya yi bayanai da dama da suke da alaka da siyasar Kano da jam'iyyar PDP a dunkule

Jihar Kano - Premium Times ta tattaro cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba ya son a kai tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 zuwa Kudancin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a daren Lahadi inda ya kuma yi magana kan matsalolin siyasa da dama gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

Tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya magantu kan batun takarar 2023
Zaben 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za ba 'yan kudu dama ba | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

A nasa muhawarar, ya yi Allah wadai da dagewar da kungiyar gwamnonin kudancin kasar ta yi a watan Yulin 2021 na cewa dole ne shugaban kasar ya fito daga yankinsu ta kowace hanya.

Ya dauki kiran da gwamnonin da sauran shugabannin suka yi a matsayin wani yunkuri na tsorata yankin Arewa domin ya sauke kudurin tsayawa takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso ya ce kamata ya yi a yanke shawarar tsayawa takara bisa dabaru ba wai ta hauragiya ko son kai ba.

Da yake kafa hujjarsa, Kwankwaso ya ce:

“Kunga mutane su na cakuda abin da bai kamata a cakuda ba. Mu na da jam’iyyu daban-daban, inda kowace jam’iyya za ta kai takara, ya ragewa dabararta.
"Idan aka yi duba zuwa 2023, jam’iyyar APC tayi mulkin shekara takwas, PDP kuma tayi 16. A cikin 16 da PDP tayi, Kudu tayi shekara 14, Arewa tayi biyu."

Kara karanta wannan

Karya ake yi mani na cewa ina shirin barin PDP, in sake komawa APC inji Rabiu Kwankwaso

A halin da ake ciki dai, jam’iyyar APC ko PDP babu wacce ta sanar da wa za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a zaben mai zuwa.

Jinkirin da manyan jam'iyun kasar biyu suka yi na tsayar da dan takara ya janyo cece-kuce kan cewa za su iya jefa tikitin ga dukkan masu son tsayawa takara.

Karya ake yi mani kan batun komawa APC

A hirar, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso yayi magana game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

A wata tattaunawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.

A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel