Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

  • Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Bulaliyar majalisar dattawan ya ce idan har jam'iyyar APC ta mika tikitinta na takarar shugaban kasa zuwa yankin kudu maso gabas toh zai yi takara
  • Sai dai ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar za ta samar da shugaban kasa wanda zai yi aiki don hadin kan kasar wanda ya fi komai muhimmanci

Abuja - Gabannin babban zaben 2023, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya bayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa.

Kalu ya ce zai duba yiwuwar yin takarar ne idan har jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mika tikinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari
Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Rahoton ya kawo cewa kungiyoyin damokradiyya da dama sun lamuncewa Kalu kuma sun nuna shirinsu na son ganin ya zama dan takarar APC a zaben shugaban kasa na 2023.

Hakazalika an gano fastocin yakin neman zaben tsohon gwamnan na Abia a manyan birane a kasar.

Kalu ya ginginawa masu son ganin ya maye gurbin Buhari

Yayin da yake nuna godiya ga kungiyoyin da ke goyon bayansa domin neman shugabancin kasar a 2023, Kalu ya bayyana cewa sun ga cewa ya cancanci jagorantar kasar ne, rahoton PM news.

Ya kuma yi martani ga fastocinsa da suka karade manyan birane a kasar sannan ya ce bai gama yanke shawarar yin takarar ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Kalu ya ce:

"Ina so na ci gaba da gode ma mutanen da suke sanya fastocina a fadin Najeriya, ban riga na yanke hukunci kan ko nayi takarar shugaban kasa ko kada nayi ba.
"Amma idan aka ba kudu maso gabas dama, zan sake tunani don ganin ko akwai kafa saboda jam'iyyar bata fadi inda za ta mika shugabancin kasar ba.
"Amma na san jam'iyyar za ta samar da shugaban kasa wanda zai yi aiki don hadin kan kasar wanda ya fi komai muhimmanci."

Babu wanda zamu baiwa tikiti cikin ruwan sanyi, APC ta maida zazzafan martani ga Tinubu

A gefe guda, jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa babu wani ɗan takarar da zata miƙa wa tikitin shugaban ƙasa a farantin azurfa cikin ruwan sanyi.

Daily Trust tace Mataimakin kakakin APC na ƙasa,Yekini Nabena, shi ne ya faɗi haka yayin da yake martani ga kalaman jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023

Bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Litinin, Tinubu yace ya sanar da shugaban kudirinsa na neman takara a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel