Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce shugaba Buhari baya adawa da burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
  • Tinubu shugaban jam’iyyar APC na kasa yana mayar da martani ne ga wata tambayar abin da shugaban ya ce bayan ya shaida masa sha’awarsa ta ya gaje shi a 2023
  • Tinubu ya ce shugaba Buhari mai bin tafarkin dimokaradiyya ne kuma ba zai ce kada ya bi burinsa da yake so a ransa ba

Abuja - Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai nemi kada ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na Legas ya bayyana hakan ne a lokacin da aka tambaye shi ko menene martanin da shugaban kasar ya mayar bayan sanar da shi aniyarsa ta tsayawa takara a 2023.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Ganawar Tinubu da shugaba Buhari
Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023 | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

An nakalto shi yana cewa:

“Wannan shine kasuwancinmu. Shi dan dimokradiyya ne. Bai nemi in dakata ba. Bai tambaye ni cewa kada in yi kokarin cim ma burina ba; buri ne na rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“To, me ya sa nake tsammanin zai ce fiye da haka? Kuna gudanar da tsarin dimokuradiyya kuma dole ne ku rungumi ka'idoji da dabi'u da kyawawan dabi'un dimokuradiyya. Shi ke nan."

Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.

Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.

A tun farko, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a gidan gwamnatin tarayya, jim kadan bayan ganawa da Buhari ranar Litinin.

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a gidan gwamnatin tarayya, jim kaɗan bayan ganawa da Buhari ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel