Babu wanda zamu baiwa tikiti cikin ruwan sanyi, APC ta maida zazzafan martani ga Tinubu

Babu wanda zamu baiwa tikiti cikin ruwan sanyi, APC ta maida zazzafan martani ga Tinubu

  • APC mai mulki tace babu wani ɗan takara da zata bi gida da tikitin takarar shugaban ƙasa a Farantin Azurfa
  • Jam'iyya mai mulki tace duk wanda ke sha'awar takara, ya zama wajibi ya bi matakai, kuma ya samu nasara a zaɓen fidda gwani
  • A ranar Litinin bayan ganawa da Buhari, Bola Tinubu ya bayyana cewa tuni shugaba Buhari ya san kudirinsa na neman takara a 2023

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa babu wani ɗan takarar da zata miƙa wa tikitin shugaban ƙasa a farantin azurfa cikin ruwan sanyi.

Daily Trust tace Mataimakin kakakin APC na ƙasa,Yekini Nabena, shi ne ya faɗi haka yayin da yake martani ga kalaman jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu.

Bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Litinin, Tinubu yace ya sanar da shugaban kudirinsa na neman takara a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

Bola Tinubu
Babu wanda zamu baiwa tikici cikin ruwan sanyi, APC ta maida zazzafan martani ga Tinubu Hoto: Eze-Orji Voicenews FB Fage
Asali: Facebook

Tinubu ya ziyarci fadar shugaban ƙasa kwanaki hudu bayan zuwan tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, kuma wasu rahoto ya nuna cewa ana zawarcinsa ne domin ya nemi takara a APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane martani APC ta yi wa Tinubu?

Da yake maida martani kan kalaman Tinubu, Nabena yace:

"APC ba zata mika tikitin ta ga kowane ɗan takara haka nan kawai ba, akwai matakai, Saboda haka zai iya cigaba da neman shawara."
"Jam'iyyar APC tana da tsari, ba jam'iyya ce da zaka zo ka ɗauka kawai ka wuce ba. Ya kamata ya nemi shawari har ga waɗan da zasu fafata a zaben fitar da gwani."
"Kowane ɗan takara ya cigaba da nazari da neman shawari, duk wanda ya samu nasara a zaben fidda gwani, shi ne zai takara a karakashin APC a zaben 2023."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Na sanar da Buhari - Tinubu

Da yake amsa tambayoyin yan jarida a gidan gwamnati, Tinubu yace ya faɗa wa shugaba Buhari muradinsa na zama shugaban ƙasa a 2023.

"Eh, na shaida wa shugaban ƙasa muradi na, amma ban sanar da yan Najeriya ba har yanzu. Ina cigaba da neman shawara ne, kuma har yanzu ban samu matsala ba."
"Ban ƙayyade iyakar mutanen da zan nemi shawarin su ba, amma nan ba da jimawa ba zaku ji abin da kuke son ji daga wurina."

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje na jihar Kano ya haramta cakuduwar maza da mata wajen ninkaya a ruwa, madugo, luwadi da sauran wasu dokoki da ya kafa.

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wasu sabbin dokoki da suka shafi Otal, wuraren cin abinci da shakatawa da kuma ɗakunan taron biki.

Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta hana shan shisha, zuwan yara Otal, luwadi da madigo da sauran su sabbij dokokin da ta sanar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bola Tinubu ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na neman takara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel