Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023

Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023

  • Dan majalisar wakilai a Najeriya ya bayyana hanyar da APC za ta bi wajen tabbatar da ta lashe zabe a 2023 mai zuwa
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana Yemi Osinbajo a matsayin dan takara nagari da kasa ke bukata
  • Hakazalika, ya bayyana wasu siffofin da mataimakin shugaban kasar ke dasu da Najeriya ke butaka a yanzu

Abuja - Wani dan majalisar wakilai, Rabaran Francis Waive ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2023 zai yi armashi ga jam’iyyar APC mai mulki idan ta tsayar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Waive wanda ke wakiltar mazabar Ughelli/Udu ta jihar Delta ya dage cewa babu wani daga jam’iyyar adawa ta PDP da zai iya kama kafar Osinbajo a 2023, Daily Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi

Dan majalisar a cikin wata sanarwa, ya yi kira ga Farfesa Osinbajo da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

Faefesa Yemi Osinbajo zai gyara Najeriya, inji dan majalisa
Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023 | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Waive wanda shine dan majalisar wakilai na APC daya tilo daga jihar Delta ya ci gaba da cewa mataimakin shugaban kasar zai lashe zaben 2023 cikin sauki a karkashin APC, Vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC da su yi abin da ya kamata tare da marawa Osinbajo baya idan har jam’iyyar na son lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Ya ce mataimakin shugaban kasar ya dauki dukkan siffofin shugaba nagari, inda ya ce ya kasance amintacce kuma mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi nuni da cewa, Farfesa Osinbajo ya tabbatar da cewa zai iya jujjuya dukiyar kasar nan, a bisa tsarin da gwamnatin yanzu ta shimfida.

Kara karanta wannan

2023: Katafaren fostan neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya karade titin Abuja

A cewarsa

"Najeriya na bukatar shugaba mai karamci kamar Osinbajo wanda ke da tunani, da yawan cudanya a fadin kasar da kuma mutunta kabilu da addinai daban-daban na kasarmu.
“Zurfin tunanin Farfesa Osinbajo, iya gudanarwa, hakuri da juriya shine abin da kasarmu ke bukata a wannan muhimmin lokaci a tarihinmu."

Don haka ya yi kira ga dukkan wadanda suka samu dama da su yi addu’a tare da yin aiki don ganin Farfesa Osinbajo ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa

A wani labarin, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Segun Sowunmi, ya bukaci Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Sowunmi, wanda ya kasance kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP a 2019, ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

Yayinda yake amsa tambaya kan wanda zai marawa baya domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, baya ga dan babbar jam'iyyar adawar Sowunmi ya ce:

"Idan an ce da zabi wani daga APC... Ina ganin Yahaya Bello zan kalla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel