Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

  • Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wani abin da zai hana shi zama shugaban kasar Najeriya na gaba a 2023
  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa wanda ya bayyana kansa a matsayin gogagge ya ce yana da ‘yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
  • Tinubu ya ce a matsayinsa na mai martaba abin da zai hana shi zama sarki (shugaban kasa) shi ne idan ya kashe mutum

Abuja - Yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.

Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bola Tinubu ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na neman takara a 2023

Ganawar Buhari da Tunubu
Bola Tinubu: Babu abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu wani abu da zai hana mai nada sarki zama sarki sai dai idan yayi kisan kai."

Tinubu ya gana da Buhari

A tun farko, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a gidan gwamnatin tarayya, jim kaɗan bayan ganawa da Buhari ranar Litinin.

A cewarsa:

"Na sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kudirina, amma ban fada wa yan Najeriya ba, har yanzun ina shawari ne."

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023

Duk da tun baya akwai alamun yana sha'awar kujera lamba Daya a Najeriya, Bola Tinubu, ya kauce wa yin kalaman da zasu nuna kudirinsa kai tsaye, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labari, an yi hira da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.

A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel