Da dumi-duminsa: Biliyan N100 ba zai isa a gudanar da zaben 2023 ba – INEC

Da dumi-duminsa: Biliyan N100 ba zai isa a gudanar da zaben 2023 ba – INEC

  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta ce naira biliyan 100 da aka ware domin gudanar da babban zaben 2023 a kasafin kudin sabuwar shekara ba zai isa ba ko kadan
  • Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a, yayin da yake kare kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin majalisar dattawa
  • Ya ce a babban zaben 2019, naira biliyan 189 aka ware don haka babu yadda za a na zaben 2023 yayi kasa

Abuja - Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce naira biliyan 100 da aka ware domin gudanar da babban zaben 2023 a kasafin kudin shekaramai zuwa ba zai isa ba ko kadan.

Yakubu ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan INEC domin kare kasafin kudin hukumar na 2022, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

Da dumi-duminsa: Biliyan N100 ba zai isa a gudanar da zaben 2023 ba – INEC
Da dumi-duminsa: Biliyan N100 ba zai isa a gudanar da zaben 2023 ba – INEC
Asali: Original

Ya ce yayin da aka warewa babban zaben 2019 naira biliyan 189, babu ta yadda za a yi na 2023 ya zama naira biliyan 100 kawai.

A ruwayar The Nation, Mahmood ya ce naira biliyan 100 kason farko ne na zaben 2023 yayin da naira biliyan 40 ya kasance kasafin kudin shekara na hukumar.

Ya ce:

"Tuni muka fara tattaunawa da ma'aikatar kudi ta tarayya kan karin bukatu don zaben 2023.
"Imma mu zo majalisar dokokin tarayya domin kare kasafin kudin a gaban kwamtin ko kuma za mu yi abun da muka yi a 2019 lokacin da bangaren zartarwa ya gabatar da kudirin ga majalisar kasa kawai mu kuma muka zo don kare shi.
"Za mu bukaci karin kudi saboda mun fadada rumfunan zabe kuma za mu gabatar da sabbin fasahohi don zabe da sauransu. Adadin masu zabe da aka yi wa rajista za su karu fiye da miliyan 84 na babban zaben 2019.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Da yake bayar da rabe-raben yadda ake son kashe kudin don zabe mai zuwa, shugaban na INEC ya ce hukumar ta ware naira biliyan 7.3 don siyan kayayyaki.

Ya ci gaba da cewa:

"Mun kuma ware naira biliyan 7 don gudanar da zabukan gwamnan Ekiti da Osun.
“Mun yi tanadin naira biliyan 2.6 ga Jihar Ekiti mai yawan mutane sama da miliyan daya da suka yi rajista da kuma naira biliyan 4.4 ga Osun mai kananan hukumomi 30.
"Za mu ware naira biliyan 4.2 don ci gaba da yin rajista a cibiyoyi 2,700 da kuma naira miliyan 619 don sa ido kan taron jam’iyyar da ayyukan yakin neman zabe.
"Ba ni da tabbacin zai isa. Muna sa ido kan tarukan jam'iyyu da zabukan fidda gwani tun daga matakin unguwanni ta hanyar wakilai. Muna da gundumomi 8,809 da jam’iyyun siyasa 18. Muna da nau'ikan zabe. Zaben fidda gwani na shugaban kasa, Sanata, Majalisar Wakilai, da na Jihohi. Idan za a yi su ta hanya wakilai, dole ne mu yi shiri don hakan.

Kara karanta wannan

Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis

“Muna da mazabun jihohi 993. Don haka, idan jam’iyyu za su zabi ‘yan takararsu, za mu sanya ido a duk wuraren da za a gudanar da zabukan - ‘yan majalisar dattawa 109, ‘yan majalisar wakilai 360 da na gwamnoni 28 domin takwas ana gudanar da su ne ba a lokacin ba. Za mu sanya ido a kan zaben fidda gwani na jam’iyya domin tantance ‘yan takara a mazabu sama da 1,400 don haka kudin zai yi yawa.
“Mun ware naira biliyan 2 don yin shari’a. Wannan ya zama babban nauyi a kan hukumar. A zabuka 27 da muka gudanar na karshe, babu wanda aka samu nasarar shari’arsa a kotu ciki har da Edo da Ondo.”

Dalilin da yasa har yanzu akwai sunayen matattun 'yan Najeriya cikin rajistar masu jefa kuri'a, Shugaban INEC

A wani labarin, hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce rashin samun sabbin bayanai kan mace-mace a Najeriya ya hana ta cire sunayen matattun ‘yan kasa daga cikin rajistar masu kada kuri’a.

Kara karanta wannan

An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma na kudi N21.9bn mai gado 14 a Aso Rock

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan bayanin a lokacin da yake zantawa da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Nasir Kwarra, a Abuja a ranar Juma'a, 24 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel