Dalilin da yasa har yanzu akwai sunayen matattun 'yan Najeriya cikin rajistar masu jefa kuri'a, Shugaban INEC

Dalilin da yasa har yanzu akwai sunayen matattun 'yan Najeriya cikin rajistar masu jefa kuri'a, Shugaban INEC

  • Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa har yanzu ba ta sabunta rajistar masu kada kuri'a ba
  • Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, a ranar Juma’a, 24 ga Satumba, ya bayyana cewa hakan ya faru ne saboda ba ta da bayanai na yanzu daga Hukumar Kidaya ta Kasa
  • A sakamakon haka, Mahmood ya bayyana cewa har yanzu akwai sunayen wasu matattun 'yan Najeriya cikin rajistar

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce rashin samun sabbin bayanai kan mace-mace a Najeriya ya hana ta cire sunayen matattun ‘yan kasa daga cikin rajistar masu kada kuri’a.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan bayanin a lokacin da yake zantawa da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Nasir Kwarra, a Abuja a ranar Juma'a, 24 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Dalilin da yasa har yanzu akwai sunayen matattun 'yan Najeriya cikin rajistar masu jefa kuri'a, Shugaban INEC
Dalilin da yasa har yanzu akwai sunayen matattun 'yan Najeriya cikin rajistar masu jefa kuri'a, Shugaban INEC
Asali: Original

Don haka, Yakubu, ya bukaci Hukumar NPC da ta tabbatar da samar da bayanan mutanen da suka mutu ga INEC don yiwa rijistan kwaskwarima.

Da yake gabatar da bukatar ga Kwarra, shugaban na INEC ya ce:

"Wataƙila kuna so ku fara da wadatar da mu da jerin fitattun 'yan Najeriya da suka mutu, ma'aikatan gwamnati da jama'ar gari waɗanda aka tattara daga bayanan ma'aikatun gwamnati, sassan da hukumomi da sauran 'yan Najeriya daga asibiti da bayanan jana'iza a duk faɗin ƙasar.
"Mun yaba da cewa wannan aiki ne mai wuya amma wannan shine dalilin da yasa muke da Hukumar Kidaya ta Kasa. Muna da yakinin cewa NPC tana da karfin yin hakan. Wannan bayanin yana da mahimmanci ga INEC don haɓaka amincin rijistar masu zaɓe ta ƙasa ”.

Kara karanta wannan

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Tsohon Shugaban INEC, Jega ya bada shawarar a kashe Jihohi 24 a Najeriya, a bar Gwamnoni 12

A wani labari na daban, tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe na kasa, Attahiru Jega, ya yi kira cewa a rage adadin jihohin da ke kasar nan domin a iya samun cigaba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa da yake magana a garin Abuja, Attahiru Jega ya bada shawarar a soke jihohi 24, ta yadda za a zauna da jihohi 12.

Farfesan ya yi wannan jawabi ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021 wajen kaddamar da tafiyar Rescue Nigeria Project wanda shi da wasu suka shigo da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel