Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babangana Umara Zulum a ranar Alhamis ya yi basaja ya kai ziyara wasu asibitocin jihar inda ya ga jami'ai na karban kudi N8,000 zuwa N10,000 duk da cewa kyauta ake jinya.

Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafinsa Gwamnan na Facebook.

Yace Zulum ya sammaci Kwamishanar Lafiyan jihar, Mrs. Juliana Bitrus, domin ta raka shi wani waje ba tare da fada mata inda zasu nufa ba.

Kai tsaye Zulum ya shiga sabon asibitin da aka gina a Gwange II dake Maiduguri kuma ya tarar ma'aikata na karban N8,000 zuwa N10,000 hannun marasa lafiya masu cuta irin Malariya kafin dubasu.

Zulum yace:

"Ma'aikatan da muka samu a nan sun tabbatar mana da cewa ana karban N8,000 zuwa N10,000 hannun marasa lafiya don basu maganin zazzabin cizon sauro. Kai har sun mayar da asibitin na kudi, shiyasa mutane basu zuwa saboda basu da kudi."

Kara karanta wannan

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

"Kawai suna amsan kudi hannun mutane suna zubawa a aljihu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya umurci hukumar kananan asibitoci ta gudanar da bincike kan lamarin kuma a hukunta ma'aikatan da aka kama da laifi.

Gwamna Zulum ya damke ma'aikata na karban kudin Haram
Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram Hoto: Governor of Borno State
Asali: Facebook

Ma'aikaci daya kacal ya tarar a asibitin

Zulum ya sake takaici yayinda ya tara da ma'aikaci daya kacal a wajen duk da cewa an dauki ma'aikata 29 aiki a asibitin kuma ana biyansu albashi.

Yace:

"Ka duba da karfe 2 na rana, wannan asibitin da muka gina da kayayyaki babu kowa cikin. Ba zamu lamunci wannan rainin hankalin ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel