Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

  • Shugaba Buhari ya ce zai bar tarihi kafin ya bar kan karagar shugabancin Najeriya a nan gaba
  • Ya ce zai kafa tarihin rufe gibin kayayyakin more rayuwa a kasar wanda ba a taba yi ba Najeriya
  • Ya bayyana haka ne ta bakin shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Gambari a birnin Abuja

Abuja - A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai rufe gibin kayayyakin more rayuwa a kasar kafin ya sauka a mulki, Leadership ta ruwaito.

Ya kara da cewa, sabanin gwamnatocin baya, za a yi amfani da rancen da gwamnatinsa ta karbo wajen gudanar da ayyuka domin rage yawan gibin ababen more rayuwa a kasar nan.

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba a Najeriya kafin ya bar ofis
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban ya yi magana ne ta bakin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a wajen bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Afirka, Dokta Bamanga Tukur mai taken 'Legacies of a Legend' a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Gambari, ya yaba da rawar da Tukur ya taka wajen yafe basussukan da ake bin kasashen Afirka, kamar dai yadda ya koka da cewa basussukan da aka ci a baya ba a kashe su ta ayyukan da suka dace na tattalin arziki ba.

Yace:

“Bashi, idan an yi kwangilar da ya dace kuma aka yi amfani da shi yadda ya kamata, muhimmin kayan aiki ne a tsarin tattalin arzikin gwamnati a fagen siyasarta.
“Shugaban mu ya kuduri aniyar aiwatar da wadannan ayyuka da kuma tabbatar da cewa kafin ya bar ofis, karkashin kulawarsa, an rage gibin ababen more rayuwa a Najeriya da aka fadada sosai.”

Da yake tunawa da irin rawar da Tukur ya taka wajen neman yafe bashi ga Afirka, ya ce:

"A karshen aiki na a can, na tuna da ayyukan Bamanga Tukur tare da Tony Blair na hukumar kula da Afirka a 2004/2005 da kuma yadda hakan ya kai ga yanke shawara mai muhimmanci a taron G8 na 2005 akan soke basussukan kasashen Afirka 32. Kafin haka, yawancin kasashe matalauta na Afirka suna amfani da wani kaso mai yawa na dan abin da suke da shi don biyan bashin."

Kara karanta wannan

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

A bangare guda, The Guardian ta ruwaito shugaba Buhari na cewa, Najeriya na bukatar dala tiriliyan 1.5 a cikin shekaru goma, domin cimma matakin da ya dace a fannin samar da ababen more rayuwa na kasa.

Ya ba da wannan adadi ne a ranar Talata a Glasgow a wani babban taron COP 26 kan inganta ababen more rayuwa na duniya wanda Shugaba Joe Biden na Amurka, Shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Von Der Leyen da Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson suka shirya.

Bashin biliyoyin dalolin kudin da ake bin Najeriya da wasu kasashe 9 ya yi yawa inji Bankin Duniya

A wani labarin, a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, 2021, Punch ta rahoto cewa Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin kasashe goma da suke fuskantar matsalar bashi.

Babban bankin Duniyan ya bayyana hakan ne a rahoton da kungiyar International Development Association ta fitar na wannan shekarar a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Rahoton kudin yace akwai wasu kasashen Duniya da ba za su iya cika yarjejeniyar da suka dauka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel