El-Rufai ya magantu kan rade-radin tasirin tsohon sarki Sanusi a tafiyar da gwamnatinsa

El-Rufai ya magantu kan rade-radin tasirin tsohon sarki Sanusi a tafiyar da gwamnatinsa

  • A yau dai El-Rufai ya yi martani kan rade-radin cewa Sanusi ne ya sanya shi sauya matsayin shugaban ma'aikatan Kaduna
  • El-Rufai ya bayyana yadda gaskiyar lamarin yake, inda ya ce ba ya neman shawarin Sanusi wajen harkokin gudanar da mulki
  • Ya bayyana cewa, ya jima dama yana tsara yadda zai sauya matsayin shugaban ma'aikatan, kuma ya samu yanzu ya yi

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karyata rade-radin cewa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sayen da yayi a majalisar zartarwa ta jihar.

El-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa a ranar 12 ga watan Oktoba a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar.

A cikin sauye-sauyen, gwamnan ya nada sabbin mukamai ga wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali zan nemi kujerar shugaban ƙasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

El-Rufai ya magantu kan jita-jitar Sanusi ne ya umarce ya kori jami'in gwamnati
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Adekeye ya ce an yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da aiki mai kyau da ci gaban gwamnati da jihar Kaduna baki daya, Leadership ta ruwaito.

Sai dai wasu da dama sun ce tsohon sarkin Kano Sanusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sauyen da aka yi, inda suka ba da misali da kalaman da ya yi a wani taro bayan da shugaban ma’aikatan gwamnan, Mohammed Abdullahi ya kira shi da tsohon sarkin Kano.

Da yake mayar da martani bayan mintuna kadan a taron da aka yi a Kaduna a watan Oktoba, Sanusi bai ji dadin maganar ba.

A lokacin Sanusi ya ce:

"Lokacin da na ji shugaban ma'aikata... Zan kira shi tsohon shugaban ma'aikata... za ku fahimci dalilin da yasa na kira ka 'tsoho' daga baya."

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

"Nan gaba kar ka kira ni 'tsohon sarki.' Babu wani abu makamancin haka."

Kwanaki El-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa, inda ya tura Mista Abdullahi zuwa ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare a matsayin kwamishina.

Bayan sukar da aka yi ta yi kan tsohon sarkin bayan da El-Rufai ya sauya matsayin Mista Abdullahi, Sanusi ya fitar da wata sanarwa cewa kalaman da ya yi kan maganar Abdullahi a kan kawai wasa ne.

Ya ce ba shi da masaniya ko hannu a sauyin da El-Rufai ya yi a majalisar kwamishinoninsa.

El-Rufai yayi bayani

Da yake magana kan wannan batu a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna a makon da ya gabata, kamar yadda gidan rediyon Liberty Hausa ya watsa, gwamnan ya musanta tasirin tsohon Sarkin a batun sauyawa Mista Abdullahi matsayi.

A cewar El-Rufai:

“Na taba karantawa a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta cewa tsohon sarki Sanusi ne ya yi tasiri wajen sake fasalin majalisar kwamishinoni. Shawara ce da na dauka tun watan Janairu. Na tattauna da dukkan kwamishinoni na, na ce musu za a yi sauye-sauye amma hakan bai samu ba sai yanzu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

“Maganar da Sarki Sanusi ya yi, wasa ne kawai ga Mista Abdullahi bayan ya kira shi, tsohon sarki. Na dauki lamarin abin ban dariya da wasa daga wadanda suke son fara wani abu daga babu.
“Khalifa Sanusi abokina ne kuma dan uwana. Shi ne shugaban jami'ar jihar mu kuma kwararre a fannin kudi. Ina yi masa magana a kan batutuwa irin haka amma ba yadda zan tafiyar da gwamnati ta ba. Ba na yin haka tare da kowa face majalisar ministocina.
“Taron da na yanke shawarar yin wadancan sauye-sauyen ya samu halartar shugaban ma’aikata kuma bai yi adawa da hakan ba. Muna so ya je ya gyara ma’aikatar ne. Matsayi ne da ya dauka a lokacin wa'adinmu na farko. Don haka zai koma can ya maido da ita yadda take a da.”

Mista El-Rufai ya kuma bayyana dalilan da ya sa ya kirkiro gundumomin gudanarwa guda uku da masu gudanar da mulki a Kaduna.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Ya kara da cewa:

“Mun samar da gundumomin gudanarwa domin saukaka harkokin mulki a yankuna uku na jihar Kaduna, Zaria da Kafanchan. Masu gudanarwa za su yi aiki a matsayin kwamishinoni."

Sauye-sauye 18 na mukamai da El-Rufai ya yi a ranar Litinin saboda wasu dalilai

A baya, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi garanbawul ga wasu mukaman jami'an gwamnatinsa ta jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana sabbin sauye-sayuen ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, an yi sauye-sauyen don ciyar da bangarori daban-daban na gwamnatin gaba.

A cikin sanarwar da ta iso hannun Legit.ng Hausa, gwamnan ya ce, an yiwa kwamishinoni takwas daga cikin 14 sauyin ma'aikatu, inda wasu kuma sauyin bai shafi su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel