Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

  • Wani mutumi da ake tunanin yana cikin kunci ya tsallake rijiya da baya a unguwar Iyana Ipaja dake jihar Legas
  • Mutumin ya hau kan hatsumiya dake cibiyar Nasfat kusa da cocin Go Yee doin kashe kansa
  • Da kyar Jami'an yan sanda, NEMA da LASEMA suka shawo kansa har ya sauko daga saman hatsumiyar

Legas - Jami'an yan sanda, NEMA da LASEMA a jihar Legas sun samu nasarar ceton rayuwar wani mutumi da ya hau saman hatsumiya da yake niyyar hallaka kansa.

Mutumin mai suna Daniel Chibuike Bassi, ya hau hatsumiyar mai tsanin zira'i 200 amma jami'an gwamnati sun tabbatar bai samu rauni ko guda ba.

Wannan abu ya faru ne ranar Laraba, 27 ga Okotoba, 2021.

Mukaddashin shugaban NEMA, reshen kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, a jawabin da ya baiwa Legit.ng yace sai da suka shawo kan Bassi kafin ya sauko daga saman hatsumiyar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas
Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas
Asali: UGC

Farinloye yace Bassi masanin aikin aluminium ne kuma yana aikinsa ne a kasuwar aluminium kuma mazaunin unguwar Dopemu ne.

Tuni dai jami'an tsaron sun garzaya da shi ofishin yan sandan Gowon Estate, Legas domin tattaunawa da jami'an NEMA.

Da alamu zautaccen mutum ne

A cewar jami'in NEMA, bisa tattaunawar da sukayi da Bassi, da alamun ya samu zaucewar hankali kuma bai iya magana sosai.

Ya kara da cewa mutumin ya gaza fadan adadin shekarunsa.

A cewar Farinloye, hukumarsa ta bukaci yan sanda su bar shi ya natsu kafin kokarin daukar wani mataki a kansa.

A cewarsa:

"Ya fada mana cewa ya isa wajen misalin karfe 0800hours kuma ya fara hawan hatsumiyar karfe 0830 hours."
"Ya bayyana cewa bai taba zuwa unguwar ba amma wani abu ne ya ingizashi zuwa wajen."

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

"Jama'a sun ce ya hau hatsumiyar ne kawai ya fara kira ga mutane su zo ayi addu'a."

Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja

A wani labarin kuwa, sakatariyar jin dadin al'umma na hukumar birnin tarayya Abuja, ta ceci wani dattijo dan shekara 56 a duniya wanda ke kokarin daukar ransa saboda kuncin rayuwar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta bayyana cewa mutumin wanda tsohon Injiniya ne karo na biyar kenan da yayi kokarin hallaka kansa.

Mukaddashin Diraktan jin dadin al'umma na ma'aikatar, Sani Amar, ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai ranar Talata a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel