Ko wane mataki PDP ta ɗauka, Zan nemi takarar shugaban kasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

Ko wane mataki PDP ta ɗauka, Zan nemi takarar shugaban kasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

  • Tsohon shugaban Sanatoci, Pius Anyim, ya bayyana shirinsa na neman tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Anyim ya bayyana cewa a baya ƙungiyoyi da dama sun nemi ya yi hakan amma ya ƙi, yanzin lokaci ya yi
  • Yace taron da PDP ta gudanar kamar an sabunta tafiyar ne, kuma alama ce ta fara harkokin siyasa gadan-gadan

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattijai, Pius Anyim, yace zai nemi tikitin shugaban ƙasa ko da PDP ta kawo kujerar yankin Kudu-Gabas ko bata kawo ba.

Sanata Anyim ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya kuma kara da cewa a yanzun jam'iyyar PDP ta ƙara karfi kuma gangamin taron da ta gudanar zai gyara komai dake faruwa.

Kara karanta wannan

Taron gangamin PDP: Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus

Sanata Anyim
Ko wane mataki PDP ta ɗauka, Zan nemi takarar shugaban kasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Meyasa zai nemi kujera lamba ɗaya?

Minsta Anyim, wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya ne, yace gangamin taron da PDP ta yi, wata alama ce ta fara harkokin siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Kungiyoyi da dama sun buga fastocin takarar shugaban ƙasa na, kuma aka watsa su a kafafen sada zumunta a 2020, amma na fito na nesanta kaina da irin wannan kiran."
"A wancan lokacin na yi tunanin ya yi wuri, domin ya dace a bar gwamnati ta maida hankali kan harkokin mulki. An sake maimata irin haka na fastoci na a 2021."
"Amma yanzun muna da ƙasa da watanni 18 zuwa babban zaɓe na gaba, saboda haka yanzun ina ganin lokaci ya yi da zan bayyana kudiri na."

Tsohon shugaban majalisa ya fito ne daga yankin kudu maso gabashin ƙasar nan, kuma ya rike wannan mukami ne a 2000 zuwa 2003, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Wane yanki PDP zata kai takara?

Anyin yace kwamitin mulkin karba-karba da PDP ta kafa ya kammala da kujerun shugabancin jam'iyya, amma bai taba sauran na siyasa ba.

"Tsarin kai wannan kujrun ya tsagaita, amma ba abinda zai hana ɗan yankin kudu maso gabas ya nemi takara, ko da kuwa ba'a kai tikiti yankin ba."
"Abu mafi alfanu shine gangamin taron da PDP ta gudanar kamar an sabunta ta ne, kuma ta fito daga cikin matsalolin da take fama da su."

A wani labarin kuma Dele Momodu ya koma jam'iyyar PDP, ya roki yan Najeriya su yafe masa kan taimakawa shugaba Buhari

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NCP, Dele Momodu, ya shiga babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Sanannen ɗan jaridan ya kuma roki yan Najeriya su yafe masa kuskuren da ya yi na bada gudummuwa har Buhari ya ɗare mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel