'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hanyar da 'yan Najeriya za su bi matsalolinsu su kau cikin sauri
  • Shugaban ya ce, 'yan Najeriya sun manta Allah shi yasa suke fuskantar kalubale iri-iri ta hanyoyi daban-daban
  • Hakazalika, Osinbajo, mataimakin shugaban kasa shi ma ya bayyana hakan a wani taron da aka yi a Abuja

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba ya ce wasu da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun yi shisshigi ga ikon Allah ta hanyar nuna rashin imani da shi dangane da rikicin kasar.

Ya yi jawabi ne a bukin buda baki na addu’o’i na kasa karo na 11 da kungiyar ‘yan majalisar Kiristoci ta kasa ta shirya mai taken “Imani a lokacin rikici.”

Kara karanta wannan

Najeriya ta zo karshe: Martanin jama'a kan yunkurin China na bude banki a Najeriya

Buhari wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin tarayya Dr Maurice Mbaeri, ya ce addu’o’i na gaskiya za su kawo canjin da ake bukata a Najeriya, The Nation ta ruwaito.

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace taken na wannan shekarar yayi magana ne karara kan halayyar wasu 'yan Najeriya wadanda suka manta da cewa Allah ne zai iya magance matsalolin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, da yawan 'yan Najeriya sun cire imani da Allah, inda suka yarda cewa dan adam ne zai iya magance musu matsalolinsu.

A bangare guda, jaridar Independent ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shi ma ya furta irin wadannan kalamai a wurin taron.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya samu wakilcin shugaban majalisar dokokin jihar Fasto Seyi Malomo, ya ce makomar Najeriya tana hannun mabiya Allah ne kamar yadda nassi ya umurce su da su rika kokawa Allah a duk lokacin da aka samu kalubale.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Shi ma ya bayyana cewa, addu'a ce za ta magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, kana kasar za ta koma daidai.

Babban Bako, Bishop David Abioye a cikin hudubarsa, ya ce imani shi ne igiyar rayuwar Kiristanci kuma abin da ake bukata don shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta.

Abioye, wanda shi ne Shugaban kuma Bishop na cocin Living Faith da ke Goshen City ta Abuja, ya ce duk da haka akwai bukatar mutane su kau da kai daga mugunta su koma ga Allah su kuma bi gaskiya.

Ya kuma kara da cewa, duk da haka, wajibi ne al’ummar kasar su ci gaba da jajircewa wajen komawa Allah.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kasar za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta ta hanyar addu’o’i.

Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce abubuwa daban-daban ne suka jawo matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

Ya yi wannan jawabi ne a wani takaitaccen biki da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, inda Jakadun Japan, Tarayyar Turai, Burundi, Denmark, Finland, Ireland, Cape Verde, Faransa, Qatar; da manyan kwamishinonin kasar Saliyo da Ghana suka karbi wasikun amincewa.

Ya ce ana bukatar karin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel