Tsohon Jigo a LP Ya Yi Wa Peter Obi Raga Raga, Ya Yi Masa Tonon Silili

Tsohon Jigo a LP Ya Yi Wa Peter Obi Raga Raga, Ya Yi Masa Tonon Silili

  • Tsohon babban jigo a jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya fito ya caccaki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi
  • Kenneth Okonkwo ya zargi Peter Obi da cin amanarsa a siyasance bayan sun yi aiki tare a lokacin zaɓen 2023
  • Hakazalika, ya nuna cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan bai da wata cancantar da zai iya yin jagoranci mai kyau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon jigo a jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya caccaki Peter Obi.

Kenneth Okonkwo ya zargi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi da cin amanarsa.

Kenneth Okwonkwo ya caccaki Peter Obi
Okwonkwo ya yi wa Peter Obi wankin babban bargo Hoto: @KennethOkwonkwo, @PeterObi
Asali: Twitter

Tsohon jigon na jam'iyyar LP ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ya yi da tashar Symfoni Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi maganganu kan Peter Obi

Kenneth Okonkwo ya ce Peter Obi ya gaza shawo kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023.

Ya bayyana cewa Peter Obi ya ɗauki ɓangaren Julius Abure a matsayin nasa, ɓangaren da ake zargin yana mu’amala da jam’iyyar APC.

Kenneth Okonkwo ya ce Obi ya ƙi amsa kiraye-kirayen da ake yi masa na nesanta kansa daga ɓangaren Abure.

Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar LP ya kuma soki salon shugabancin Obi, yana cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ba shi da halayen aiki da ƙungiya ko shugabanci mai tasiri.

Ya kawo wasu misalai da ke nuna cewa Obi ya taɓa goyon bayan ƴan takarar da ba na jam’iyyar LP ba a lokacin zaɓe, wanda hakan ya sa masu biyayya ga jam’iyyar suka ji an ware su.

“Da muka fara tafiyar a 2023, tafiya ce ta gaskiya. Kowane ɗan Najeriya na buƙatar sauyi. Kowa bai gamsu da yadda abubuwa ke tafiya ba. Don haka muka ga wani sabon haske yana bayyana a gaba."
“Kuma saboda ni mutum ne da ke da kishin tsaro da jin daɗin ƴan Najeriya, ba wai ɗan siyasa da ke da biyayya ga kowace jam’iyya ba, na rungumi tafiyar da zuciyata. Ba wanda ya tursasa min shiga."

“Na bi tafiyar da kaina. Don haka da aka zaɓe ni a matsayin mai magana da yawun tafiyar, na girmama wannan dama. Kowa ya san abin da na yi da gudummawar da na bayar.
“Mun yi abin da muka yi, kuma mun gaskata cewa mun ci zaɓe. Me ya biyo baya? Idan kai ƙwararren ɗan siyasa ne, abin da ya kamata ka fara yi shi ne ka fara shiri da ƙarfafa jam’iyyarka don 2027, kuma jam’iyyar ce mafita ta farko."

- Kenneth Okonkwo

Kenneth Okonkwo ya yi maganganu kan Peter Obi
Okonkwo ya ce Peter Obi ya ci amanarsa Hoto: @KennethOkonkwo
Asali: Twitter

Okonkwo ya zargi Peter Obi da cin amana

Tsohon jigon na jam'iyyar LP ya bayyana Peter Obi a matsayin ɗan siyasa wanda bai da alƙibla.

"Babu wanda ke kashe wa Obi tafiyar siyasarsa. Obi ne ke kashe siyasarsa da kansa."

- Peter Obi

Kenneth Okonkwo ya ƙaryata zargin cewa ya ci amanar Obi ne ta hanyar barin jam’iyyar LP.

"Duk ɗan siyasar da ya san abin da yake yi, ba za a iya cin amanarsa ba. Idan akwai wanda ya ci amanar ɗan uwansa, to zan iya faɗa da ƙarfi cewa Peter Obi ne ya ci amanata."

- Kenneth Okonkwo

Ƴan siyasan da ke haddasa rikici a LP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure, ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Julius Abure ya wanke gwamnatin Shugaba Bola Tinubu daga zargi kan haddasa rikici a jam'iyyar LP.

Shugaban na LP ya zargi tsohon ɗan takarar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, tare da gwamnan Abia, Alex Otti, da haddasa dukkanin rikicin da ke addabar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng