Bidiyo: Amarya Ta Tubure Gaban Iyaye, Ta Fasa Zuwa Gidan Miji bayan An Daura Aure

Bidiyo: Amarya Ta Tubure Gaban Iyaye, Ta Fasa Zuwa Gidan Miji bayan An Daura Aure

  • Wani bidiyo da ya bazu a intanet ya nuna wata amarya tana kuka, tana nuna cewa ba za ta je gidan mijinta ba yayin da ake lallashinta
  • Amaryar da ake kira Hauwa ta dage cewa ba za ta bar gidansu ba, tana cewa "ku bar ni in mutu a nan," duk da lallashin 'yan uwanta
  • Mutane sun yi martani kan bidiyon, wasu suna zargin auren dole ne, yayin da wasu ke cewa za ta sauya ra’ayi idan aka ce an fasa auren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A wani bidiyo da ya jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, an ga wata budurwa da ake kyautata zaton amarya ce ta ki yarda a kaita dakin mijinta.

Amaryar wacce ke sanye da hijabi kuma zaune dirshan a jikin wata mata da ke lallashinta, ta nuna sam ba za ta rabu da iyayenta ta tafi gidan miji ba.

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

An ga bidiyon amarya tana cewa ba za ta je gidan miji ba
Bidiyo ya nuna lokacin da wata amarya ta ce ba za ta je dakin mijinta ba. Hoto: Anadolu / Contributor
Asali: Getty Images

Amarya ta ki yarda a kai ta gidan miji

A cikin bidiyon da wata Mufeeda Wada ta wallafa a shafinta na X, an ga amaryar tana kuka tana cewa ita ba za ta tafi ba, sai dai a barta ta mutu a gidansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaryar da aka ji wata mata daga wajen bidiyon ta kirata da suna Hauwa ta ce:

"Ku kyale ni in mutu a nan, wallahi ba zan tafi ba."

Amarya Hauwa dai ta dage da cewa "ni ba zan je" yayin da iyaye da 'yan uwanta da ke a cikin dakin suke ci gaba da ba lallashinta.

Yayin da amaryar ke rusar kuka, matan da ke cikin dakin sun ci gaba da lallashinta a kan ta tashi ta kai ta dakin mijinta.

'Yan soshiyal midiya sun yi martani

Wannan bidiyo ya jawo ce-ce-ku-ce a sohiyal midiya, musamman a sashen sharhin wacce ta wallafa bidiyon, inda mutane suka bayyana ra'ayoyinsu.

Kara karanta wannan

'Munafurcin siyasa ba na irinmu ba ne': El Rufai ya sake ta da kura, ya jaddada matsayarsa

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin wadanda suka kalli wannan bidiyo:

@bapphah:

"Sai su ba shi daki a nan, tun da ya biya."

@zeeboy72:

"Ina jin auren dole ne."

@i_bamalli:

"Ku bar ta kar ta tafi, idan aka kwana biyu da kanta za ta tafi."

@Ouumar_Faruk:

"Haba, rabu da ita, da ta ji muryar baba za ta tashi."

@SaleemAbdu88526:

"Irin su ne idan an kai su ba sa son zuwa gida ziyara."

@khaleed_kwamee:

"Ku ce mata za a fasa auren ku ga in bata sheka da gudu ba, munafurcin banza."

Kalli bidiyon a nan kasa:

Amarya ta rasu ranar da aka daura aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa an shiga tashin hankali a Kano bayan da wata amarya Hannatu Yahaya ta rasu jim kadan bayan an daura aurenta.

Wani matashi mai suna Gen Sunusi ya bayyana labarin a shafukan sada zumunta, yana mai cewa amaryar ta rasu kafin ta kai gidan mijinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.