Wani Uba Ya Yi Watsi da 'Yan Kai Amarya, Ya Yi Wa Diyarsa Rakiya Zuwa Dakin Mijinta da Kansa, Bidiyo

Wani Uba Ya Yi Watsi da 'Yan Kai Amarya, Ya Yi Wa Diyarsa Rakiya Zuwa Dakin Mijinta da Kansa, Bidiyo

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wani uba da ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta
  • Mahaifin amaryar bai jira an kawo motoci da sunan kai amarya ba, ya bukaci mahaifiyarta da yayarta su zo su yi masa rakiya don kai ta gidan angonta
  • Angwanai na cikin kokarin hada motocin da za su yi jerin gwano don kwaso 'yan kai amarya, sai kawai suka ga mahaifinta ya taso keyarta a gaba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Kamar yadda aka saba bisa al'adar Mallam Bahaushe da mutanen Arewa, a duk lokacin da aka ce za a kai amarya dakin mijinta, 'yan uwa da abokan arziki kan taru su yi mata rakiya.

Kara karanta wannan

"Ba ta siyarwa bace": Uba ya mayarwa ango da kudin sadakin diyarsa, ya yi magana 1 mai ratsa zuciya

Mutanen Arewa tun zamanin baya suna mutunta wannan al'ada, inda a kauyukan karkara akan yi wa amarya rakiya ta hanyar yin wake-wake da sauransu.

Uba ya raka diyarsa dakin mijinta da kansa
Wani Uba Ya Yi Watsi da Yan Kai Amarya, Ya Yi Wa Diyarsa Rakiya Zuwa Dakin Mijinta da Kansa Hoto: @el_bonga
Asali: Twitter

Sai dai kuma, wani uba da aka yi auren diyarsa a kwanan nan, ya yi watsi da wannan al'ada, inda ya zabi aiki da koyarwar addini a madadin haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo da shafin @el_bonga ya wallafa a X, mahaifin amaryar ya zabi mahaifiyarta da yayarta domin su yi mata rakiya zuwa dakin mijinta.

Matashin ya bayyana cewa yayin da suke ta cuku-cukun hada motoci domin zuwa dauko amaryar da 'yan kai amarya sai kawai suka yi karo da mahaifinta, mahaifiya da yayarta sun kawo ta dakinta.

Ya yi wa bidiyon take da:

"Yayin da muke tsare-tsaren hada motoci don yin jerin gwano wajen kawo amarya gidanta kamar yadda yake bisa al'ada, kwatsam, mahaifinta ya ba kowa mamaki ta hanyar kawota da kansa tare da matarsa da yayarta."

Kara karanta wannan

"Tsoho ya dawo": Karamin yaro ya fashe da dariyar jin dadi yayin da ake yi masa susan kunne

Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani bayan uba ya kai diyarsa dakin mijinta

@alhajiji1987 ya ce:

"Ci gaba mai kyau da kayatarwa. An hutar da kowa.
"Amma Mallam Bonga, wai kunya ce ke sa su rufe fuska? Bayan duk mun gama ganin fuskokin a Instagram da Twitter da Facebook? Lol"

@KaitafiS ya yi martani:

"Abin da surukina ya yi mani kenan shekaru 13 da suka wuce."

@Usman_M_Isah ya ce:

"Sak abin da ya faru kenan a ranar aurena. Ina hada mutanena xaaje dakko amarya sai dai kawai aka kirani akace ai ga mata ta can surukina dina ya kawo ta. Nace Alhmdlh, baba ya rage mana aiki."

@Zaynab_Adamm ta ce:

"Ina rokon Allah yasa mahaifina ya yi mani irin haka."

Uba ya mayarwa ango kudin sadakin diyarsa

A wani labarin kuma, mun kawo cewa daya daga cikin bidiyoyi mafi shahara a TikTok a yan kwanakin nan ya nuno wani uba 'dan Najeriya wanda ya bai wa dangin ango mamaki ta hanyar mayar masu da kudin sadakin da suka biya na auren diyarsa.

Mahaifin amaryar, wanda ya kasance Bayarabe, ya yi bayanin cewa a al'adarsa mayar da kudin sadakin amarya, wata alama ce ta girmamawa da godiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel