Kperogi da IBK: Maganar Sanusi II kan Tinubu Ta Jawo Muhawara Mai Zafi a Arewa
- Kalaman mai martaba Muhammadu Sanusi II kan manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu sun jawo muhawara mai zafi a Arewa
- Farfesa Farooq Kperogi ya zargi Sarki da goyon bayan manufofin da suka kuntatawa talaka, yana mai kwatanta maganarsa da abin ban dariya
- A daya bangaren, Farfesa Ibrahim Bello Kano (IBK) ya mayar da martani, yana kare Sanusi II tare da zargin Kperogi da hassada a kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kasance a tsakiyar ce-ce-ku-ce kan manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wani jawabi da ya gabatar a Lagos, Sarkin ya ce ba zai taimaka wa gwamnati wajen kare manufofin da yake ganin sun dace ba, saboda yadda ya ji an nuna masa rashin kulawa.

Asali: Facebook
Lamarin ya ja hankalin marubuta kuma Farfesoshi, Farooq Kperogi da Ibrahim Bello Kano (IBK), inda suka yi musayar ra'ayi mai zafi kan matsayin sarkin da irin halayensa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Farfesa Kperogi ga Sarki Sanusi II
A cikin wani rubutu mai tsawo da ya yi a ranar Asabar, Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa Sarkin Kano yana nuna son kai.
Farfesa Farooq Kperogi ya ce;
“Sarkin ya goyi bayan manufofin tattalin arzikin Tinubu, amma ya ki kare su saboda ba a nuna masa kulawa ba.”
Kperogi ya kara da cewa irin wannan hali ya saba wa mutuncin da ake tsammanin daga manyan shugabanni.
Ya ce sarkin ya kare manufofin cire tallafin mai da karya darajar Naira, wadanda suka jefa talakawa cikin kunci.
Farfesa IBK ya kare Sanusi II
Farfesa Ibrahim Bello Kano ya mayar da martani ga Farfesa Kperogi, ya kare matsayin Sarkin Kano.
Ya ce Kperogi ba shi da cikakkiyar masaniya kan halayen Sanusi II, tare da zargin cewa hassada ce ta sa ya caccake shi.
Farfesa IBK ya bayyana cewa;
“Kperogi ba ya iya jure ganin mutane masu hangen nesa da kuma masu daukaka kamar Sarkin Kano.”
IBK ya kuma yi suka ga rubutun Kperogi, yana mai cewa ya dogara ne kacokam kan hassada da neman kawo nakasu ga martabar Sanusi II.
Ya kara da cewa, Kperogi ya fi mayar da hankali kan neman gyara wadanda suka fi shi martaba maimakon yin adalci ga batutuwa.
Ra’ayoyin jama’a kan takaddamar
Ra’ayoyin jama’a sun kasu kashi biyu, inda wasu ke goyon bayan Kperogi yayin da wasu ke tare da IBK.
Mubarak Ibrahim Lawal ya wallafa a Facebook cewa;
“Wannan ce-ce-ku-ce ya nuna gwanintar Kperogi da IBK a rubuce-rubuce. Ya kamata daliban harshen Ingilishi su bi wannan tattaunawa domin koya daga basirarsu.”
A bangare guda, Gimba Kakanda ya yi suka ga IBK a kafar Facebook, yana mai cewa:
“Martanin IBK ya kasa nuna zurfin ilimi, kuma ya yi amfani da kalaman nuna kabilanci da rashin dacewa.
"Ya kamata IBK ya gabatar da hujjoji masu karfi maimakon zargin Kperogi da hassada.”
A daya bangaren kuma, masu sharhi da dama sun goyi bayan Farfesa IBK suna masu cewa abin da ya fada a kan Farfesa Kperogi gaskiya ne.
Tattaunawar da ake bugawa tsakanin Kperogi da IBK ta jawo hankalin masu karatu da dama, musamman masu sha’awar harshe da adabi.
Haka zalika ta nuna yadda manufofin gwamnati ke shafar rayuwar jama’a, da kuma irin martanin da suke a kan lamarin.
Sarautar Kano: Shehu Sani ya kawo mafita
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bukaci a buga kwallo tsakanin bangaren Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Shehu Sani ya ce hakan zai kawo karshen takaddama da ake a kan sarautar Kano ta inda duk wanda ya yi nasara a kwallon ya zama sarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng