Shehu Sani Ya Kawo Hanyar Sasanta Aminu Ado da Sanusi II a wajen Kotu
- Sanata Shehu Sani ya ba da shawarar magance rikicin Masarautar Kano ta hanyar wasan kwallon kafa maimakon ci gaba da kai ruwa rana a kotu
- Shehu Sani ya ce duk wanda ya yi nasara a wasan zai zama sarki kai tsaye, yana mai cewa zai iya zama alkalin wasa yayin da za buga wasan
- Biyo bayan bayanin, jama’a sama da 2,000 sun tofa albarkacin bakinsu game da shawarar, inda wasu suka yaba, wasu kuma suka soki ra’ayin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya fito da wata shawara mai ban mamaki kan yadda za a magance rikicin masarautar Kano.
Maganar Sanatan na zuwa ne yayin da kotun daukaka kara ya yanke hukunci kan shari'ar da ake bugawa tsakanin bangaren Aminu Ado Bayero da gwamnatin Kano.

Asali: UGC
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanatan ya shawarci masu martaba Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero su fice daga kotu su fuskanci juna a filin kwallo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Shehu ya ce wasan kwallon kafa tsakanin masu gardama kan kujerar sarautar zai zama hanya mai sauƙi wajen gano wanda ya kamata ya hau gadon masarautar.
Yadda za a warware rikicin sarautar Kano
Leadership ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani ya fadi hanyar da za a warware rikicin sarautar Kano a cikin wani sakon barkwanci da ya jawo ce-ce-ku-ce.
“Mai martaba Aminu Bayero da Mai martaba Sanusi su janye ƙara daga kotu. Dukansu su zaɓi 'yan wasan kwallon kafa daga Kano domin su fafata a filin wasa na Sani Abacha."
“Sarakunan biyun su zama kyaftin na bangarorinsu, yayin da zan iya zama alkalin wasa domin ina da alaƙa da yankunan Bebeji da Bichi."
"Duk wanda ya yi nasara tsakanin ƙungiyar Aminu FC ko ƙungiyar Sanusi FC zai zama sarki kai tsaye. Nagode.”
- Shehu Sani
Ra’ayoyin jama’a kan shawarar Shehu Sani
Bayan wallafa sakon, mutane da dama sun bayyana ra’ayinsu a kan wannan shawara ta Sanata Shehu Sani.
Yunus Musa Sulaiman ya ce;
“Idan za a bi wannan shawara, to ya kamata a ce wannan dabarar ta yi aiki tsakanin kai da Oga Nasir El-Rufai a lokacin neman tikitin takarar gwamnan Kaduna."
Bashar Almustapha kuwa ya bayyana rashin goyon bayansa ga shawarar, yana mai cewa;
“Wannan shawara ba ta dace ba, cikin girmamawa, ba ta da ma’ana. A ganina, Aminu Ado Bayero ya kamata ya yi hakuri domin gwamnati ba ta goyon bayansa.
"Kuma hakan zai taimaka wajen zaman lafiya a jihar Kano da Arewa baki ɗaya.”
Shitu Ahmed Obassa ya yi watsi da shawarar, yana mai cewa;
“Wannan ra’ayi ba zai yi aiki ba. Irin wannan ba a taba yin shi ba a tarihin Hausawa ko Fulani ba, musamman a Kanon Dabo.
"Ya kamata a kyale wannan batu, domin siyasa ce ta sa wannan rikicin ya gagara karewa.”
Tinubu ya yi raddi ga Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi raddi ga mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II game da ba ta bada shawara.
Fadar shugaban kasa ta yi Allah wadai da kalaman da Sanusi II ya yi a kan tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu yayin wani taro a Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng