"Ina da Mafita amma ba Zan Taimaka ba," Sarki Sanusi II Ya Yi wa Shugaba Tinubu Tatas
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimakawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gyara kura-kuran da ta yi a tsare-tsarenta ba
- Sarkin Kano ya bayyana cewa duk da yana da abokai a gwamnatin amma ba su ɗauke shi a matsayin aboki ba saboda yadda suke mu'amalantarsa
- Duk da an maido da shi sarauta, ana zargin gwamnatin tarayya ta ci gaba da goyon bayan magabacinsa, Mai martaba Aminu Ado Bayero
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa ba zai taimaka wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen gyara manufofin da ke illata al'umma ba.
Sarki Sanusi ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba a Lagos, lokacin da ya jagoranci taron cika tunawa da fitaccen lauyan nan Gani Fawehinmi karo na 21.

Asali: Twitter
Ya ce akwai abubuwan da zai yi bayanin kuskuren da aka yi da yadda za a gyara don kaucewa shiga wani hali amma ya zaɓi ya tsame hannunsa, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Sarki Sanusi II ba zai taimaka ba?
Basaraken ya bayyana cewa ya zaɓi ya kama bakinsa ba tare da taimakawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba saboda yadda take mu'amalantarsa bai masa daɗi ba.
"Ina da abubuwan da zan faɗa game da tattalin arziki, waɗanda suka yi bayanin halin da muke ciki da yadda aka hango shi tun farko, galibi za a iya magance su amma ba zan faɗa ba."
"Na zaɓi na kama baki na daina yin magana kan tattalin arziki ko gyare-gyare domin idan na bude baki na yi magana, hakan zai amfanar da wannan gwamnati, ni kuma ba na son taimaka mata."
- Sarki Muhammadu Sanusi II.
Babu nagartattun mutane a gwamnatin Tinubu
Sanusi II ya ƙara cewa duk da yake yana da abokai a cikin gwamnatin Tinubu amma yadda ba su nuna halin abokantaka ya sa shi ma ya kama kansa.

Kara karanta wannan
Ana shirin ƙara farashin fetur a Najeriya, NNPCL ya tara wa gwamnati Naira tiriliyan 10
A ruwayar Channels tv, Sarkin ya ƙara da cewa:
"Ba su da mutane nagartattu da za su su yi wa ƴan Najeriya bayani, ni dai ba zan taimaka ba, da farko na fara haska masu amma yanzu na tsame hannu na."
"Su ya rataya a kansu su fito su yi wa ƴan Najeriya bayanin dalilin da yasa suka aiwatar da manufofinsu."
Sarki Sanusi II ya hango halin da za a shiga
Duk da haka, ya ce halin da ake ciki a yau ba sabon abu ba ne, domin an riga an yi hasashen faruwar hakan shekaru da dama da suka gabata.
“An gargadi mutane shekarun da suka shige cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, za a kawo wannan matakin, amma suka rufe idonsu suka ƙi yin abin da ya kamata," in ji sarki.
Sanusi, wanda aka tsige daga sarautar Sarkin Kano a 2020 lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya koma kan sarauta a 2024 bayan NNPP ta karɓi mulki.
Har yanzu sarautarsa tana fuskantar ƙalubale daga gwamnati mai mulki a tarayya, wacce har yanzu ake ganin ta na goyon bayan magabacinsa, Aminu Ado Bayero.
Ɗaya daga cikin lokutan da ake zargin gwamnatin tarayya tana tare da Aminu Ado shi ne lokacin Nuhu Ribaɗo ya kira shi da sarkin Kano a wurin wani taro a Abuja.
Sanusi II ya yi magana kan hukuncin kotu
Ku na da labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya buƙaci Kanawa su dage addu'ar samun zaman lafiya da kariya da fitintinu.
Sanusi II ya yi wannan magana ne yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke game da rikicin sarautar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng