Kudin fetur: An yi daidai da aka cire tallafin mai Inji Sanusi Lamido Sanusi

Kudin fetur: An yi daidai da aka cire tallafin mai Inji Sanusi Lamido Sanusi

- Muhammadu Sanusi II ya ce cire tallafin man fetur abu ne mai matukar kyau

- Tsohon Sarkin ya ke cewa mutanen Najeriya za su ga amfanin wannan mataki

- Sanusi II ya kuma yabawa gwamnatin APC na daidaida farashin shan lantarki

Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cire tallafin man fetur.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na karin kudin shan wutar lantarki da man fetur abu ne mai kyau.

Ganin halin tattalin arzikin da aka shiga a sakamakon annobar COVID-19, Malam Sanusi II ya ce ya kamata a gane gwamnati ba sadaka ta fito yi ba.

KU KARANTA: Man fetur: An soki Buhari bayan ya kamanta farashin Saudi da Najeriya

Jaridar Punch ta rahoto Muhammadu Sanusi II ya na cewa gwamnati ba za ta iya cigaba da abin da ta ke a kai mai kama da ‘rabon goron kirismeti’ ba.

Sanusi II ya ce: “A dalilin annobar COVID-19, tattalin arzikin Najeriya ya durkushe, ina tunanin yanzu dole Najeriya ta fuskanci ainhin halin da ake ciki.”

“Mu na biyan biliyoyin daloli da sunan wani tallafi. Damfara ce kurum wanda aka yi shekaru 30 ana yi.” Inji tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan.

“A ‘yan watannin bayan nan, gwamnati ta kawo gyare-gyaren da idan aka cigaba da tafiya a haka, za a kai ga ci. Cire tallafin man fetur ya na cikinsu.”

KU KARANTA: Najeriya ta kashe makudan kudi wajen biyan tallafin fetur

Kudin fetur: An yi daidai da aka cire tallafin mai Inji Sanusi Lamido Sanusi
Shugaba Buhari Hoto: Channels TV
Asali: UGC

“Daidaita farashin man fetur daya daga cikinsu ne.” Sanusi II ya yabawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ya ce dama ace tun tuni aka yi wannan.

“Wadannan gyare-gyare da ya kamata ayi. Mu na bukatar mu fahimci cewa gwamnati ba ta da karfin da za ta cigaba da wannan sadaka da kudi."

Kwanakin baya kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana a kan ƙarin kudaden lantarki da man fetur da gwamnati ta yi.

Ya ce babu maganar biyan tallafin man fetur a cikin kasafin kudin da ta aikawa majalisa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel