Sallah: Hukumar Tace Fina Finan Kano ta Kafa Kwamitin Tsaftace Ayyukan Gidajen Wasanni

Sallah: Hukumar Tace Fina Finan Kano ta Kafa Kwamitin Tsaftace Ayyukan Gidajen Wasanni

  • Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano ta kafa kwamitin tsaftace shagulgula a gidajen wasanni yayin bukukuwan sallah
  • Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ya kafa kwamitin ne domin ganin gidan wasannin ba su gudanar da wasannin da za su ci karo da addini ko al'ada ba
  • Kwamitin, wanda aka kafa a yau Litinin zai bibiyi gidajen wasannin da kuma kai rahoto ga hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano - Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano ta kafa kwamiti na musamman wanda zai lura da yadda gidajen wasanni a Kano suka gudanar da shagul-gulan bikin karamar sallah.

Kara karanta wannan

"Za mu waiwayi bidiyon dala": Abba ya magantu kan shekara 8 na mulkin Ganduje a Kano

Jami'in Hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya tabbatarwa legit Hausa cewa hukumar, Abba El-mustapha ne ya kaddamar da kwamitin a yau Litinin karkashin jagoranci daraktan kudi da mulki na hukumar, Abdulkarim Badamasi.

Sallah: Hukumar tace fina-finai ta Kano ta kafa kwamiti da zai hana ayyukan badala a gidajen wasannin dake jihar
Hukumar tace fina-finai ta Kano ta samar da kwamitin tace ayyukan gidajen wasanni Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

El-Mustapha ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da bin doka da dakile duk wani abu da ake tunanin zaici karo da al'adah ko tarbiyar addinin musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba El-mustapha a cikin sanarwar ya ce:

"Aikin kwamitin shi ne zagayawa gidajen wasannin domin lura da su tare da kawowa Hukumar rahoto kan yadda suka gudanar da shagulgulan bikin sallar."

Hukumar fina-finai ta ja kunnen kwamitin

Abba El-Mustapha ya kuma yi kira ga wanda aka zabo a matsayin yan kwamitin su mayar da hankali a kan aikin da aka ba su.

Ya hore su da kawo rahoton da ake bukata domin tsaftace ayyuka gidajen wasannin.

Kara karanta wannan

Tuhuma kan aikata laifuffuka 26, Emefiele ya isa kotu, ya gurfana gaban alkali

Kano: Za a hukunta wanda ya karya doka

Abba El-mustapha ya lashi takobin tabbatar da an hukunta duk wani gidan wasan da aka samu da laifin karya doka.

Daga cikin hukunce-hukuncen fa gidajen wasannin da aka samu da laifi za su iya fuskanta akwai ƙwace lasisin sa na dindindin.

Hukumar fim ta hukunta mai saɓa doka

A baya, kun ji hukumar ta dakatar da jarumin finafinan kannywood, Abdul Saheer na shekaru biyu saboda sabawa dokoki da ka'ida.

An zargi wannan tauraro da wallafa bidiyo mai ɗauke da batsa a shafukansa na sada zumunta wanda hakan ya jawo abin magana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel