Kano: Hukumar Tace Fina Finai Ta Bada Dalilan Dakatar da Jarumi Na Shekaru 2

Kano: Hukumar Tace Fina Finai Ta Bada Dalilan Dakatar da Jarumi Na Shekaru 2

  • Abdul Saheer ya gamu da fushin hukumar tace fina-finai, hakan ya jawo an dakatar da shi daga shiga fim a Kano
  • Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha ya zargi jarumin da wallafa bidiyon banza da kin bayyana a gabansu
  • ‘Dan wasan kwaikwayon da aka fi sani da Malam Ali a Kwana Casa’in ya ce bidiyon da ya yada bai da alaka da batsa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta laftawa Abdul Saheer haramcin duk abin da ya shafi harkar fim har na shekaru biyu.

A wani bidiyo da aka samu a tashar rediyon Freedom, Abba El-Mustapha ya yi cikakken bayanin abin da ya sa su ka dauki matakin.

Kara karanta wannan

Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

Shugaban hukumar ta Kano ya zargi jarumin da aka fi sani da Malam Ali a shirin Kwana Casain da wallafa bidiyo mai dauke da batsa.

Malam Ali Kwana Casain
An dakatar da Malam Ali Kwana Casain daga fim Hoto: Arewa Media da Abba El-Mustapha1
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Ali bai amsa gayyata ba

Malam Abba El-Mustapha ya fadawa taron manema labaran cewa sun gayyaci Abdul Saheer domin ya iya kare kan shi a gaban hukumarsu.

A cewar El-Mustapha, Malam Ali (Kwana Casa’in) bai amsa wannan gayyata ba, a karshe dole hukumar tace fina-finan ta zartar da hukunci.

Shugaban da aka fi sani da Abba na Abba ya ce kin bayyana a gaban hukumar tamkar raina mutanen jihar Kano ne da kuma mutuncinsu.

An raba Malami Ali da sha'anin fim

Leadership ta ce El-Mustapha ya ja-kunnen ‘yan jarida su guji yin hira da Abdul Saheer a kan duk wani abin da ya shafi harkar fim a jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da su ka taimaki APC, suka Kashe LP da PDP a zaben Gwamnan Imo

A karshe, ya bukaci masu shirya wasannin kwaikwayon da su ka shirya wasa dauke da Abdul Saheer su kawo fina-finansu domin a duba su.

Hukumar za ta duba wadannan fina-finai ne na makonni biyu, da zarar wa’adin ya cika, El-Mustapha ya nuna za su dauki mataki mai tsauri.

Malam Ali ya wallafa bidiyo na batsa?

Sai dai mutane sun ce bidiyon da ya jawowa ‘dan wasan matsala bai dauke da batsa kamar yadda hukumar tace fina-finan Kano ta ke zargi.

Da alama watsi da gayyatar da aka yi masa ya jefa sa a matsala. A wani bayaninsa a tashar Freedom, Saheer ya musanya laifin da aka jefa masa.

El-Mustapha ya rasa mahaifiyarsa

Kwanakin baya aka samu labari cewa Mahaifiyar shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ta riga mu gidan gaskiya.

El-Mustapha ne ya sanar da labarin rashin da ya yi a ranar Talata, 29 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel