Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
An yi sulhu tsakanin Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo). An yi hakan bayan Oshiomhole ya zargi Akpabio da karya yarjejeniya.
Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya fara yajin aiki a jihohin da ba su fara biyan sabon mafi karancin albashi ba. Ta ba gwamnonin jihohin wa'adi.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan halayen wasu alkalai da ke hukuncin zalunci inda ya ce su tuna ranar da Allah zai tsayar da su a ranar gobe.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasa su amfani da iliminsu wajen kawo ci gaba a Najeriya, su guji neman dama waje. Ya ce gwamnati ta zuba jari mai yawa a iliminsu.
SERAP ta nemi Shugaba Tinubu ya dakatar da Wike da gwamnoni daga bayar da kyautar motoci da gidaje ga alkalai, tana jaddada cewa hakan na iya tauye fannin shari'a.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ba da gudunmawar kudi ga iyalan mutanen da 'yan bindiga suka kashe. Gwamnan ya bukaci mutane su ci gaba da ba da hadin kai.
Ministan Gidaje Yusuf Abdullahi Ata ya ce babban burinsa a matsayin minista shi ne dawo da Kano ga APC a 2027, yana mai godiya ga Tinubu kan nadin da aka yi masa.
NDLEA ta dakile yunkurin shigar da miyagun kwayoyi zuwa Biritaniya, an gano su cikin huhun gyada da aya. An kara tunatar da jama'a duba kayayyaki a filin jirgi.
Mukaddashin hafsan sojojin kasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya isa jihar Sokoto biyo bayan bullar 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa.
Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya taya sabon shugaban Amurka, Donald Trump murnar zama sabon shugaban kasa bayan kammala zabe.
Labarai
Samu kari