Tsagin jam'iyyar PDP da ke karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, ya gabatar da dan takarar gwamna a Gombe. Hakan na zuwa ne an ba Pantami takarda.
Tsagin jam'iyyar PDP da ke karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, ya gabatar da dan takarar gwamna a Gombe. Hakan na zuwa ne an ba Pantami takarda.
Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa yan bijilanti ne a bidiyon da ake yadawa na wasu mutane na wucewa kusa da jami'an a kan babura a jihar Katsina.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar kama wani boka da ake zargi yana ba 'yan bindiga masu fashi da makami maganin bindiga a jihar Akwa Ibom ranar Juma'a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyukan Suwa da Ding’ak a Mushere, Bokkos a Plateau, inda suka kashe mutum uku ciki har da Fasto.
‘Yan sandan Kaduna sun kama mutane uku a Soba da Giwa, sun kwato bindigogi 8 da babura 4 na sata, tare da dakile ayyukan ta’addanci da barna a jihar.
Wasu rahotanni sun ce ana zargin wani kwamandan Bello Turji da ake kira Duna Sani da kisan mutane da dama, yanke kan mata da cin zarafin mata da munanan laifuffuka.
Gwamnatin Kano ta soke kwangilar titin Jaba-Gayawa bayan bidiyon Dan Bello da ya nuna yadda titin ya lalace. An kuma amince a kashe N14.8bn kan manyan ayyuka.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta saki dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a yammacin Juma'a. Sowore ya yi godiya bisa wadanda suka tsaya masa wajen ganin ya fito.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya saba jawo cece-kuce kan irin matakan da yake dauka a gwamnatinsa. Na baya-bayan nan shi ne umarnin kulle gidan rediyo.
Shugaban kunguyar IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima ya tabbatar da cewa matatar Ɗangote ta kara N30 a farashin kowace lita da take sayarwa ƴan kasuwa.
Peter Obi ya ba da N15m ga kwalejin jinya da makarantar islamiyya a Bauchi, yana yabawa rawar malaman jinya tare da alkawarin tallafa musu a fadin kasa.
Labarai
Samu kari